Majalissar Dattawan Najeriya ta tabbatar da Alkali Tanko Muhammed a matsayin babban alkalin alkalan Najeriya bayan da ya yi rikon kwaryar wannan mukamin kusan tsawon watanni shida.
A yau Laraba, Majalisar ta tabbatar mai da mukamin.
An haifi alkali Tanko Mohammed ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1953 a garin Doguwa da ke karamar hukumar Giade a jihar Bauchi a Arewacin Najeriya.
Ya yi makarantar gwamnati da ke Azare ta sakandare, kuma ya kammala a shekarar 1973. Sannan ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Daga baya ya yi karatun Majistrate a shekarar 1984, da kuma digirin-digirgir duk a Jami'ar Ahmadu Bello a shekara 1998.
Shugaba Buhari ya nada Justice Tanko a matsayin mai rikon kwarya a watan Janairu bayan da ya dakatar da tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnoghen wanda aka zarge shi da boye kaddarorinsa.
Facebook Forum