Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dattawan Arewa Sun Nemi Fulani Makiyaya Su Koma Arewa


Kungiyar Dattawan Arewa
Kungiyar Dattawan Arewa

Farfesa Abdullahi ya yi wannan kira ne inda ya yi ikrarin cewan ba za a ba su kariya ba saboda ka'idar da gwamnonin shiyyar kudancin kasar suka samar  wa makiyaya, da ke cewa sai dai su rika diban dabbobinsu a mota amma ba dai su yi kiwo a kasa ba.

Kungiyar Dattawan Arewa ta yi Kira ga Fulani Makiyaya da ke kudancin kasar da su koma Arewa.

A daidai lokacin da jam'iyyar adawa ta PDP ke kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa dokar ta baci a bangaren tsaro, Kungiyar Dattawan Arewa karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ta yi kira ga dukanin makiyaya da ke kudancin kasar, da su tattara nasu 'inasu su koma Arewa.

Abdullahi ya yi wannan kira ne inda ya yi ikrarin cewan ba za a ba su kariya ba saboda ka'idar da gwamnonin shiyyar kudancin kasar suka samar wa makiyaya, da ke cewa sai dai su rika diban dabbobinsu a mota amma ba dai su yi kiwo a kasa ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi binciken abubuwan da ke faruwa saboda a yi wa kowa adalci idan za a biya diyya bayan sun dawo gida.

Sai dai daya daga cikin shugabannin Gammaiyar Kungiyoyin Matasan Arewa Sherrie Nastura Ashir, ya ce an sha yin irin wadannan tarurukan tun a zamani Marigayi Abacha, amma kuma duk ba su yi wa kasa amfani ba.

Yanzu kiran da suke yi shi ne, a kafa Kwamitin raba gardama, saboda duk wanda yake so ya zauna a Najeriya a ba shi dama ya zauna a duk inda yake so.

A lokacin hada wannana rahoton dai fadar shugaban kasa ba ta ce komai akan wannan lamari ba.

A saurari rahoton wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda Daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG