Karar da wani lauya mai suna Donald Okonkwo ya shigar, ya hada da Ofishin Jakadancin kasar Ingila, da shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, da kuma Ministan Shari'a na Kasa.
Donald Okonkwo ya ce ya shigar da karar ne saboda a yi maza a dawo da Nnamdi Kanu ya fuskanci shari'a, saboda hare haren da haramtacciyar Kungiyar sa ta IPOB ta kai akan mutanen.
Daga cikin wadanda IPOB ta kai wa hari a 'yan kwanakin baya, akwai tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ike Ekwerenmadu a kasar Jamus. Sanan kuma kungiyar ta ci gaba da barazanar damke shugaban kasa Muhammadu Buhari, da a yanzu haka ya ke kasarJapan da kuma Gwamnoni da wasu manyan mutane da ke tafiye tafiye zuwa kasashen waje daga Najeriya.
A lokacin da yake nazari akan batun shigar da karar Barista Mainasara Ibrahim Umar ya ce duk da cewa shigar da irin wanan kara hurumi ne na Ministan Sharia, amma babu dokar da ta hana 'dan Kasa mai kishin kasa ya dauki irin wannan mataki.
Asali ma kungiyar da wanan shugaba na IPOB ke tinkaho da ita, haramtacciya ce., kuma akwai dokokin da suka bada hurumin a dawo da duk wani wanda yake kulla ta'addanci, a duk wata kasa kamar yadda shi Nnamdi Kanu yake aikatawa da bata wa kasa suna.
Ibrahim Musa sakataren wata kungiya da ke sa ido akan harkokin cin hanci da rashawa da bada shugabanci mai kyau, wato a turance Global Watch Against Corruption and Bad Leadership Initiative, ya ce hujojjin da wannan lauya ya bada a lokacin da ya shigar da karar abu ne mai kyau. Amma da ya shigar da karar a Majalisar Dinkin Duniya, da ya fi ma'ana domin akwai wasu take-take da kasar Ingila ke yi a fagen diplomaciya.
Amma mai fashin baki a al'amuran yau da kullum, kuma dan jarida mai zaman kansa Bashir Baba, ya ce lallai dawo da Kanu Najeriya yana da muhimmanci saboda yana ci gaba da bata wa kasa suna a duk kasar da ya tafi, domin Kanu ya zamar wa Najeriya annoba.
Tunda aka bada belin Nnamdi Kanu a shekara 2018 ne, ya gudu zuwa kasar Isra'ila, daga baya kuma aka ganshi a cikin kasar Ingila inda yake gujewa shari'a da Gwamnatin Tarraiya.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda.
Facebook Forum