Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Soke Umurnin Dakatar Da Hukumar DAAR Communications


Kotun Tarrayya da ke Abuja karkashin shugabancin mai Shari'a Inyang Ekwo, ta soke umurnin dakatar da hukumar DAAR Communications, masu gidan Radiyon Raypower da AIT Talabijin, da hukumar kula da kafofin watsa shirye shirye ta kasa tayi.

Wannan ya biyo bayan shigar da kara ne da shugaban hukumar DARR Communications Raymond Dokpesi ya yi a kotu akan matakin dakatar da gidajen watsa labaran.

An dakatar da lasisin DAAR Communications ne har zuwa wani lokaci da hukumar NBC ba ta kaiyade ba.

Sakataren hukumar NBC Mohammed Mujtaba Sada, ya bada hujjojin yadda gidan labaran ya karya dokokin gudanar da aiyukan su. Sada ya ce an yi kokari samun sulhu da kamfanin, amma kokarin bai yi ba, shi ya sa aka dauki matakin dakatar da su kamar yadda doka ta tanada.

Amma kungiyar 'yan jaridu ta kasa NUJ, ta bakin sakataren ta Shuaibu Leman, ya ce matakin da hukumar NBC ta dauka bai yi dadi ba, inda kungiyar ta yi kira da a gaggauta soke wannan dokar, saboda Demokradiya ta cigaba da samun muryar 'yancin yin magana a lokacin da ya dace.

Sai dai wata kungiyar matasa mai kare muradun 'yan kasa mai suna YPN wato "Youth Project Nigeria," a cewar sakataren ta Yahuza Abubakar Karshi, ya ce matakin da hukumar NBC ta dauka akan kamfanin DAAR Communications ya yi daidai.

Saboda kamfanin baya bin dokokin kasa sannan kuma kamfanin na tauye wa ma'aikata sa hakkokin su. Yahuza ya ce bayan nan ma kamfani ya kori ma'aikata dari 500 ba tare da biyan hakkokinsu ba.

Abin jira a gani shine ko hukumar NBC za ta bi umurnin kotu wajen janye dakatar da DARR Communications ko za ta daukaka kara.

Medina Dauda ta aiko muna da wannan rahoton..

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG