Tuni har an riga an yi masa karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai, kuma idan wanan kuduri ya samu shiga, Majalisa za ta iya tilasta Shugaban Kasa da Gwamnoni su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyin da aka bijiro masu a duk lokacinda bukatar hakan ta taso.
Majalisar Wakilai ta kawo wani kudurin da zai ba Majalisar karfin ikon gayyatar Shugaban Kasa da Gwamnonin Jihohi zuwa gabanta domin su amsa tambayoyi akan gudanarwa idan bukatan haka ta taso.
A karon farko a tarihin Majalisar Dokokin Najeriya an samu salo na yawan kwanakin da Majalisar za ta rika zama don yin dokoki da za su kara kawo ci gaba a kasa.
Bisa dukkan alamu dai, hukumomi a Najeriya sun yi amai sun lashe akan farashin man fetur da suka sha alwashin ba za a kara shi a wanan wata na Maris ba.
Sarakunan kasa sun mika kokensu ga kwamitin Majalisar Dattawa da zai yi wa kundin tsarin kasar garambawul a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo Agege, inda suka nemi a mayar masu da ikon da tsarin mulki ya basu a baya.
Masana harkokin tsaro sun koka dangane da yawan mutanen da aka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa a wannan shekara ta 2021. Bisa kiyasi, daga watan Janairun 2021 zuwa karshen Fabarairu, an sace mutun sama da 1,000.
Wasu cikin mata da ke karkashin Gamayyar Kungiyoyin Mata ta Najeriya a karkashin jagorancin Madam Gloria Laraba Shoda sun yi kira ga Gwamnati da ta karfafa hukumomni tsaro don magance yawan sace sacen dalibai da ake yi a makarantu.
A yayin da kasashe da dama a duniya ke kokarin fara amfani da tsarin sadarwa na 5G, Najeriya ma ba a bar ta a baya ba duk da yake al'amarin yana fuskantar suka daga wasu a kasar.
Sababbin shugabanin hukumomin tsaro da Majalisar Dattawa Najeriya ta tantance sun yi alkawarin za a samu sauki a matsalar tsaro da ke addabar Kasar nan ba da jimawa ba.
Biyo bayan sace dalibai da malaman makarantar kimiyya ta gwamnati da ke Kagara a jihar Neja, Majalisar Dattawa na kira ga shugaban kasa ya gaggauta ayyana dokar ta baci a fannin ilimi.
A Najeriya Majalisar dattawa ta ce ta samu takardar bukatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika mata mai dauke da sunan Abdurashid Bawa wanda zai zama sabon shugaban hukumar EFCC.
Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci gwamnan babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, don ya yi wa kwamitocin ta bayani game da dakatar da amfani da kudaden yanar gizo na zamani mai suna cryptocurrency.
Babban Bankin Duniya ya amince da shirin baiwa Najeriya bashin Dalar Amurka Miliyan 500 domin ta inganta samar da wutar lantarki da kuma fadada hanyoyin sadarwa na kamfanonin rarraba wutar lantarki.
Ministan ayyuka da gidaje na Najeriya Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a Abuja inda ya ce an amince da yin manhajar yanar gizo ta zamani da za ta bada dama a rika kula da ayyukan kwangilolin kan titina da kuma sa ido kan titinan su kansu.
Yayin da kwararru ke tabbatar da zargin karuwar cin hanci da rashawa a Najeriya, ita kuwa gwamnatin kasar karyata zargin ta yi.
A Najeriya rikici ne ya ke neman kunno kai a jam'iyyar APC mai mulki lamarin da ya kai ga wasu sanannun 'yan jam'iyyar suka fara kokawa da yadda shugaban jam'iyyar mai rikon kwarya kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ke tafiyyar da jam'iyyar.
Akwai bukatar kowane jami'in kasar ketare ya samu lambar zama dan kasa ta wucin gadi a Najeriya.
A Najeriya, Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya bada umurnin a rufe Babban Ofishin Hukumar Bada katin Dan kasa wato NIMC domin dakatar da cincirindon Jama'ar da ke taruwa a hedikwatar hukumar a kowace rana da zummar samun lambar zama dan kasa.
Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ta hanzarta dakatar da batun rajistar lambar zama dan kasa, NIN idan har ana so a samu saukin hauhawar sabbin kamuwa da cutar coronavirus.
A Najeriya, Ministan sadarwa da tattalin arziki ta hanyar zamani, Isa Ali Pantami, ya fada jiya cewa za a iya hada katinan SIM guda 7 da lambar shedar dan kasa daya.
Domin Kari