Farashin man fetur din dai a yanzu yana lilo a tsakanin kudin da ake sayar da shi a da a Naira 162.50 da kuma na yanzu tsakanin Naira 180 zuwa Naira 200, har Naira 212 duk da alwashin da hukumomin suka dauka a makkoni biyu da suka gabata na cewa ba za a kara ba.
A lokacin da Muryar Amurka ta zanta da Shugaban ma'aikatan man fetur na Najeriya, Mele Kolo Kyari ya ce akwai man fetur har lita miliyan dubu biyu da ma'aikatar ta ke da shi a kasa kuma babu niyyar karin kudin man fetur a wanna wata na Maris.
Karin bayani akan: Minista Timipre Sylva, man fetur, Mele Kolo Kyari, Nigeria, da Najeriya.
A halin da ake ciki yanzu wasu ‘yan Najeriya suna kokawa da hawan farashin man fetur ya kai har Naira 200. Wasu kuma sun ce sai sun yi zagaye suna neman mai amma da kyar ake samu a gidan mai akan farashin da ya banbanta da wanda Gwamnati ta kaiyade.
Wakiliyar Muryar Amurka ta zagaya cikin garin, don tabbatar da wannan al’amari kuma ta tarar da dogayen layi, da yan bunburutu suka yi katutu a kofar gidajen man fetur, suna sayar da shi a jerka lita 10 a farashin Naira 3000, lita ashirin kuma Naira 6000, da abinda ya dara haka.
Wannan hasashe na karin farashi dai, yayi ta reto a tsakanin hukumomin da ke da alhaki akan sha'anin man fetur, inda har Minista Timipre Sylva da kansa,ya bada sanarwa da ta nuna alamun akwai bukatar farashin ya karu, ko ba a yanzu ba, idan aka yi la'akari da hidindimu na samarwa da kuma daidaita farashin na man fetur.
Saurari rahoton Medina Dauda cikin sauti: