Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya sanar da samun wasikar shugaban kasa Mahammadu Buhari inda ya bada sunan Abdurashid Bawa daya daga cikin ma'aikatan Hukumar da ya kama aiki tun shekarar 2005.
Majalisar za ta tantance shi kafin a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar kamar yada majalisar ta saba yi.
Shi Abdurashid Bawa dan shekara 40 ne, tabbatar da shi zai nuna cewa shi ne mutum na farko da zai shugabanci Hukumar wanda bai ta6a yin aikin dan sanda ba, sa6anin yadda ake yi a baya.
Shugaban Kungiyar yaki da cin hanci da rasahwa ta kasa da kasa, Transparency International reshen Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani ya yi tsokaci cewa a baya an yi zargin Abdurashid Bawa da almundahana a lokacin da yake gudanar da aikinsa, duk da cewa ba a tabbatar da laifi akan sa ba, yana fata in an tantance shi zai rike aiki cikin gaskiya.
Amma tsohon Ministan Matasa da wasanni Barista Solomon Dalung ya ce aiki ne babba a gaban matashin, inda ya bada shawara cewa sai ya rika tuntubar manya saboda ya samu alkiblar tafiyar da aikin sa tare da fatan kuruciya ba za ta fi karfin zuciyar sa ba.
A lokacinda yake nashi nazarin, wani matashi kuma mazaunin birnin taraiyya Abuja, Umar Mohammed Gombe ya ce wanan nadi da shugaba Mohammadu Buhari yayi zai samu nasara domin tun lokacin da aka kafa EFCC a shekara 2005 an nada Nuhu Ribadu, matashi dan shekaru 43 an yi ta samu cigaba, amma daga baya sai aka nada wadanda shekarun su suka wuce 50, sai ci baya aka rika samu. Umar Gombe ya yaba da wanan mataki inda yake cike farin ciki da annashuwa yana cewa yaki da cin hanci da rashawa zai sama nasara sosai fiye da yadda aka saba gani.
Idan Majalisar Dattawa ta tantance Abdurashid Bawa zai karbi ragamar hukumar EFCC daga hannun Mohammed Umar wanda yayi rikon hukumar tun watan Yuli na bara da aka dakatar da Ibrahim Magu kan zargin almundahana.
Saurari rahoton a cikin sauti daga Medina Dauda:
Karin bayani akan: EFCC, Abdurashid Bawa, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.