Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Garkuwa Da Sama Da Mutane Dubu Daya A Najeriya Bana-Kwararru


Masana harkokin tsaro sun koka dangane da yawan mutanen da aka yi garkuwa da su domin neman kudin fansa a wannan shekara ta 2021. Bisa kiyasi, daga watan Janairun 2021 zuwa karshen Fabarairu, an sace mutun sama da 1,000.

Kwararrun sun nuna cewa a wannan shekara an samu labarin satar mutane fiye da 450 a arewa maso yammacin Najeriya, sai kuma a yankin arewa ta tsakiya inda aka sace mutane kusan 479.

Duk da haka ana ganin cewa akwai mutane da dama da aka dauke a jihohi musamman irinsu Neja, Sokoto, Zamfara, da Katsina ba tare da an samu labari ba. Yankunan da ake da karancin wannan matsala su ne kudu maso gabas da kudu maso kudu.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dakta Yahuza Ahmed Getso, masanin harkar tsaro kuma mai bin diddigi kan yadda ake aikata laifuka, ya ce wannan adadi shi ne wanda aka sani amma akwai wadanda suke wuraren da jami'an tsaro ba sa kaiwa balle har su iya sanin yawan wadanda ake sacewa. Dakta Getso ya ce akwai jan aiki a gaban hukumomi domin ya kamata su gano wurin da kudaden da ake biyan 'yan ta'addan ke fitowa, sannan wa ake ba kudin?

Masanin harkar tsaro ya ce, abinda ya ke kara daure masa kai shi ne yawan kudaden da masu garkuwa da mutane ke karba, wanda idan aka yi kiyasi za a samu sun wuce Naira biliyan 10 a wannan dan tsakanin. Dakta Getso ya ce mahukunta suna da laifi kwarai da gaske domin ya kamata su tafi da zamani wajen yin amfani da na'u'rori masu aiki da kwakwalwa don gane yadda ake biyan wadannan 'yan ta'adda kudade.

To sai dai ga Manjo Bashir Galma Mai ritaya, ya fi ganin batun a zargin da ake yi wa mutanen da ke zaune a wadannan wurare da ake yawan sace-sacen al'umma, wajen kin bayyana sunayen 'yan uwansu da ke yin wannan mumunar sana'ar ta yin garkuwa da mutane. Manjo Bashir ya ce mahukunta su yi hobbasa wajen samar wa matasa ayyukan yi. Sannan a dage da yi wa al'umma adalci wajen zamantakewa domin a rage yawan kwadayi da ke sa mutane cikin halin kunci har su kai ga aikata laifi.

Kuwarrarun sun ce manyan hanyoyi da masu garkuwa da mutane suka fi yin ta'asa sun hada da Benin-Ore, Benin-Auchi-Okene, Keffi-Akwanga da kuma titin Akure-Owo. Hanyoyin Arewa da suka zama tarkon 'yan bindiga kuma su ne Abuja-Lokoja, Zaria-Sokoto-Gusau sai Bauchi-Tafawa Balewa, Wukari-Takum da kuma Mina-Kontagora.

Sauri cikakken rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG