Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Kungiyar Likitoci Ta Nemi Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Aikin Rijistar Katin Zama Dan Kasa


Tambarin hukumar NIMC
Tambarin hukumar NIMC

Kungiyar Likitoci ta Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ta hanzarta dakatar da batun rajistar lambar zama dan kasa, NIN idan har ana so a samu saukin hauhawar sabbin kamuwa da cutar coronavirus.

Wannan kira ya biyo bayan yadda jama'a ke tururuwa kullum zuwa ofisoshin hukumar NIMC yin rajistar katin zama dan kasa, ba tare da bin ka’idojin da aka gindaya na kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus ba.

Shugaban kungiyar likitoci ta kasa, Farfesa Innocent Ujah, ya ce bai ga wani dalili da zai sa gwamnati ta nemi a yi rajistar katin zama dan kasa yanzu ba, duba da yadda ake fama da annobar cutar coronavirus.

Farfesa Ujah, ya ce abin da ya kamata a yi shi ne a fuskanci yadda za a iya shawo kan cutar da ke ta kara bazuwa domin a yi kokarin dakile ta.

Amma ga babbar jami'a a Hukumar Ayyana Zama dan Kasa, Hajiya Hadiza Ali Dagabana, ta na ganin dakatar da aikin yin rijistar ba zai yi wa kasa kyau ba, domin a cewar ta akwai kwararan dalilai da suka sa aka fara yin rajistar tun shekarar 2015.

Hadiza Ali, ta ce ya zuwa yanzu suna da wadanda suka riga suka yi rajista har miliyan 44 a cikin rumbun su, kuma idan aka yi la'akari da yawan masu lambobin waya a kasa da suka kai miliyan 85, to yanzu ne aka kusan yi wa rabin su rajista.

Daya daga cikin matasan da suka je cibiyar domin yin rajista, Saidu Ibrahim, ya bayyana ra'ayinsa cewa akwai alamun karancin ma’aikata a cibiyar, shi ya sa ake dadewa ba a yi wa mutum rajista ba.

Saidu ya bada shawarar cewa kamata ya yi gwamnati ta yi saurin kai dauki ga hukumar wajen kara yawan ma'aikata.

Wannan batu na rajistar katin zama dan kasa na daukar hankalin yawancin hukumomin gwamnati domin a yanzu haka hukumar Kare Hadura ta kasa FRSC, karkashin jagorancin Boboye Oyeyemi, ta bada umurnin cewa nan da yan watanni mutum ba zai iya rajistar abin hawa ba sai da katin zama dan kasa.

Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG