Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudurin dokar Ikon Gayyatar Shugaban Kasa Gaban Majalisa Na Janyo Takaddama


Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari.

Tuni har an riga an yi masa karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai, kuma idan wanan kuduri ya samu shiga, Majalisa za ta iya tilasta Shugaban Kasa da Gwamnoni su bayyana a gabanta domin amsa tambayoyin da aka bijiro masu a duk lokacinda bukatar hakan ta taso.

A daidai lokacinda Majalisar dokokin Najeriya ke haramar yi wa Kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, Majalisar Wakilai ta kawo wani kudurin da zai ba ta karfin ikon gayyatar Shugaban Kasa da Gwamnonin Jihohi zuwa gabanta domin su amsa tambayoyi akan al'amuran gudanarwa idan bukatar haka ta taso.

Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Sokoto Dokta Abdullahi Balarabe Salame ya ce wannan doka dama babu ita a cikin kundin tsarin mulki da ta yi bayani karara cewa ana iya kiran Shugaban Kasa zuwa gaban Majalisa, amma akwai abinda ake kira resolution a Turanci. Saidai Dokta Salame ya ce dokar ba ta da wani alfanu koda an yi dokar saboda tana iya kawo yamutsi a harkar gudanarwa saboda Kundin tsarin Mulki ya rarraba wa ko wane sashi aikin da ya kamata ya yi. Abdullahi Salame ya ce akwai muhimmin aiki da aka ware wa bangaren Majalisa baya ga yin doka, shi ne sa ido a bangaren zartaswa. Saboda, haka wannan doka ba za ta yi wani amfani ba.

Karin bayani akan: Shugaban Kasa da Gwamnonin, Majalisar Wakilai, Majalisar Dattawa, Shugaba Muhammadu Buhari​, Nigeria, da Najeriya.

A lokacin da yake nashi nazari, Sanata Mai wakiltar Nasarawa ta Yamma, Abdullahi Adamu ya ce wannan kudurin doka bai riga ya isa Majalisar Dattawa ba tukuna. Sanata Abdullahi Adamu ya ce abu ne mai wuya irin wannan kudurin ya samu karbuwa a Majalisar Dattawa domin daga dukan alamu akwai wani nufi da wadanda suka kawo kudurin suke da shi, kuma ba nufi ne mai kyau ba tunda Kundin tsarin mulki ya raba wa kowane bangare aikinsa. Wani bangare ba zai shiga na wani ba,saboda a samu cigaba mai dorewa.

Amma ga tsohon dan Majalisar Dattawa daga Jihar Kaduna ta tsakiya Kwamred Shehu Sani kafa irin wannan doka ba laifi ba ne domin za ta ba Majalisa dama ta yi aikin ta yadda ya kamata, kuma kasa za ta fi samun amfani idan har ana amfani da dokokin yadda aka tsara su, ba tareda nuna fifiko ko son rai ba.

Kokarin gyara dokar da 'yan Majalisar ke yi ya samo asali ne tun daga lokacin da Majalisar Wakilai ta nemi bayyanar Shugaban Kasa a zauren ta amma kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami ya gabatar da jinkiri da ya hana yin hakan.

Ga Medina Dauda da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00


XS
SM
MD
LG