Ministan sadarwa da tattalin arziki ta hanyar zamani Isa Ali Pantami, ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya ke hira da gidan talabijin din Channels mai zaman kansa a Abuja.
Ya fadi cewa sun kirkiro wata manhaja da ke da yanar gizo wacce za ta sauwaka wa mutune yin wannan rajistar matukar mutum ya na da lambarsa ta zama dan kasa da ake kira NIN a takaice.
Pantami ya ce shi ya sauke manhajar mai suna Global Line a yanar gizo ta hanyar Google wanda za a iya amfani da ita kai tsaye.
Minista Pantami ya kuma ce ma'aikatan hukumar bada katin dan kasa sun koma bakin aiki kuma za su ci gaba da ba 'yan kasa hadin kai wajen sama musu lambobin NIN.
Ita kuwa darakta a hukumar bada katin zama dan kasa Hajiya Hadiza Ali Dagabana, ta ce a kwanan nan wasu kamfanoni da hukumar ta basu lasisi da izini, za su fara yawo sako-sako domin yi wa 'yan kasa rajista a sauwake.
Gwamnatin taraiyya ta ce masu yin amfani da layin waya da NIN su na da zuwa ranar 19 ga wannan watan na Janairu, su hade lambar NIN dinsu da katin SIM.
A yayin da masu neman rajista ba tare da NIN ba suke da har zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu na wannan shekara.
Ya zuwa watan 10 na bara, jimlar yawan layukan tafi da gidanka ko salula ya kai kusan miliyan 208 a Najeriya amma a halin yanzu 'yan Najeriya miliyan 44 ne kachal ke da lambar NIN, saboda haka masu amfani da wayar hannu miliyan 164 ne za su yi kokarin hada layukan su da lambobinsu na NIN.
Saurari karin bayani cikin sauti:
Karin bayani akan: NIN, Isa Ali Pantami, Nigeria, da Najeriya