Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Yi Amfani Da Tsarin Sadarwa Na 5G Wajen Shawo Kan Matsalar Tsaro A Najeriya - Pantami


Isa Ali Pantami.
Isa Ali Pantami.

A yayin da kasashe da dama a duniya ke kokarin fara amfani da tsarin sadarwa na 5G, Najeriya ma ba a bar ta a baya ba duk da yake al'amarin yana fuskantar suka daga wasu a kasar.

Alamu sun fara bayyana a kan shirin Najeriya na fara amfani da tsarin sadarwa na 5G a matsayin kokarin bin rukunin kasashen da tuni suka fara amfani da shi a duniya.

Wannan ya fito ne daga bakin Ministan Sadarwa na Najeriya Dr. Isah Ali Pantami a lokacin da yake karin haske ga manema labarai a kan wannan yunkurin na ma’aikatar sa, musamman saboda korafe-korafe da suka kunno kai a kan illar fara amafani da tsarin sadarwa na 5G.

Tun shekaru biyu da suka wuce jama'a suka fara waiwayar illolin da ke akwai a harkar sadarwar 5G, inda aka rika bayanai daban-daban da ke nuna babu wata illa sai ma ci gaba da Najeriya za ta samu a bangaren sadarwa.

Minista Pantami ya jadadda cewa hukumomin duniya a bangaren sadarwa ITU da kuma Kiwon Lafiya WHO sun fitar da sakamakon bincike da ya nuna babu wata illa.

Dr. Isah Ali Pantami ya ce an fara da 2G aka koma 3G, sai 4G kuma duk ci gaba ake samu.

Sannan ya kara da cewa turirin zafin da wayoyi suke amayarwa wato radiation na 4G ya ma fi na 5G din, har ma da na'uran dumama abinci wato microwave da tukunyar busar da gashi ta hair dryer da mata ke amfani da su, duk sun fi na 5G.

Saboda haka mutane su kwantar da hankalinsu a cewar Pantami, domin amana ce wadda gwamnati ta dauka na kare lafiyar al'umma, kuma ba za ta yi wasa da ita ba.

Minista Dr. Pantami ya kara da cewa muhimmin manufan Ma'aikatar Sadarwa na tura wannan tsari shi ne na ganin an yi amfani da wannan hanyar sadarwa ta zamani wajen shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Sai dai kuma Malami a Jami'ar Abuja kuma mai fashin baki a fanin zamantakewan dan Adam, Dr. Farouk Bibi Farouk, ya ce akwai abin dubawa a binciken da ma'aikatar sadarwa ta ce ta yi musamman a kan wannan tsarin sadarwa na 5G domin Najeriya ba ta da kimiyyar gano illar wannan tsari.

“Akwai hanyoyi da dama da ya kamata a gwada nasara ko rashin ci gaba da gwamnati take samu musamman a fannin abubuwan more rayuwa, wadda a halin yanzu akasin haka ake samu a Najeriya” in ji Bibi Farouk.

Farouk ya kara da cewa babu tsaro, ba bu motoci da aka saya na daukan mara lafiya zuwa asibiti a cikin lokaci, sannan kuma yana ganin Ministan Sadarwa ba zai iya tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za a samu masu cin hanci da rashawa a fanin tafiyar da tsarin ba.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00


Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG