Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Fulani Da Ke Aikin Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Koya Wa Mata 200 Sana'o'in Hannu A Nasarawa


Kayayyakin da aka koya wa mata hadawa a wajen taron.
Kayayyakin da aka koya wa mata hadawa a wajen taron.

Kungiyar Fulani ta Walidra da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Najeriya ta koya wa mata fulani 200 sana'o'i hannu a Rugan Julie da ke karamar hukumar Karu ta Jihar Nasarawa domin taimaka masu su samu dogaro da kansu daga mawuyacin halin da yan bindiga suka jefa yawancin su a ciki.

Wadannan mata 200 sun koyi sana'o'i iri daba-daban har 21 da suka hada da yin man gashi, sabulun wanka da na wakin mota har da magani kashe kwari da wanda za a tsaftace ruwan wanka da shi da sauran sabulai daban-daban da ake amfani da su a ayyuka cikin gida.

Daya daga cikin matan, Murjanatu Mohammed ta bayyana ra'ayin ta a yaba da wannan horo na koyon sana'o'i da aka koya musu.

KUNGIYAR MATA
KUNGIYAR MATA

Murjanatu ta ce wannan sana'a da ta koya ya ba ta karfin gwiwa na dogaro da kanta, domin za ta sayar da abubuwan da ta sarrafa da kanta saboda samun kudin yin amfanin yau da kullum.

Ta kuma yi kira ga yan'uwanta mata da su fito su koyi sana'o'i da zai taimaka wa rayuwar su har ma su amfani wasu.

A lokacin da ta ke na ta nazarin Hajiya Hauwa Abdullahi Ardo, wacce ita ce ta ke koya wa mata wadannan sana'o'i ba tare da tallafi daga ko ina ba, ta bayyana wa Muryar Amurka abin da ya sa ta yi wanna hobbasa din

Hauwa ta ce hali da aka tsinci kai a ciki a yau musamman ma Fulani da yanzu haka sun zama masu gudun hijrah a wurare daban daban, shi ne ya sa ta ga ya dace ta fito ta koya wa mata sana'a domin su dogara da kansu.

Ta kara da cewa sayar da nono ne mace ta ke alfahari da shi, to yanzu babu shanun balle har ta samo nono ta tatsa don sayarwa. 'Yan ta'adda sun tarwatsa su.

Shi kuwa Shugaban Kungiyar Fulani ta Walidra, Yusuf Musa Ardo ya ce ya kafa Kungiyar ne domin taimakekeniya wa al'umman fulani wadanda suke shiga halin ha'ula'i a sakamakon rashin tsaro da ya afka masu har suka rasa yanayin rayuwa na kiwo da noma.

Yusuf ya ce burin sa shi ne mata da yara wadanda sune aka fi musgunamawa a lokuta irin wanda kasa ke ciki, su samu ayyukan yi, saboda hankalin su ya dawo wuri daya.

A lokacin da ya ke jawabin goyon baya ga wannan shirin, Sarkin Hausawa na Mararraban Gurku a karamar Hukumar Karu na Jihar Nasarawa Adamu Usman Mani, ya ce wannan mataki da aka dauka na koya wa mata sana'a abu ne na tallafa wa al'umma baki daya, domin dogaro da kai zai hana ta'addanci.

Adamu ya ce shi mai goyon bayan wanan yukuri ne kuma zai ba da goyon baya saboda cibiyar koyar da sana'ar ta bunkasa sosai har ta yadu a jihar Nasarawa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


XS
SM
MD
LG