Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoton ENDSARS: Wata Karyar Ce Kawai Aka Tsara Inji Gwamnatin Najeriya


Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed (Twitter/@FMIC)
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed (Twitter/@FMIC)

A karon farko tun bayan fitowar rahoton da Kwamitin Endsars na jihar lagos ya gabatar, Ministan Yada Labarai da al’adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed ya maida martani a madadin Gwamnatin Tarayyar Najeriya, inda ya yi watsi da rahoton a matsayin labaran karya da aka tsara su.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya fara da cewa abin mamaki ne yadda aka tattara irin wadannan zarge zarge na karya da wasu ‘yan Najeriya suka yi kawai aka gabatar da su a matsayin rahoton kwamiti da aka kafa domin binciken zargin cin zarafn ýansanda.

Lai ya ce ba a ta6a fitar da wani rahoto mai dauke da labaran karya, da kutungwila, da zukitamalle har da kazafi irin wannan rahoton ba.

Lai ya ce abin mamaki ne, a ce irin wannan Kwamiti da ke dauke da masana harkar shari’a kuma kwararru su fito da irin wannan sakamako cike da karya da kurakurai, sa6ani da hasashe, da zarge zarge a matsayin rahoto bincike. Wannan ya nuna cewa ba su yi wani bincike ba, kawai sun maimaita abubuwan da ke yawo a dandalin sada zumunta ne da ba a tantance ba tun faruwar lamarin a ranar 20 ga watan Oktoba na shekara 2020, sa6anin dalilin da ya sa aka kafa su tun farko.

Lai ya ce kwararru sun yi bayanin cewa nazarin yanayin wadanda aka kai su cibiyoyin kiwon lafiya 5 na nuni da cewa babu wani harsasai na soja da ya samu wani cikin masu zangazanga a tashar Lekki a ranar 20 ga watan Oktoba a cikin lokutan 6.30 na yamma zuwa karfe 9 saura minti 26 na dare. Saboda haka karya ce aka yi cewa sojoji sun harbi wadansu a wurin.

Ministan ya ce a binciken da Kwararren likita Forfesa John Obafunwa ya yi akan Gawarwaki uku da aka samu, daya ne kawai ke dauke da alamun harbi, kuma “ba harsashin sojojinmu ba ne.”

Lai ya ce ,inda an kashe mutane kamar yadda rahoton ya baiyana, ina iyayen wadanda aka kashe su ke? Me zai sa su ki fitowa su nuna bakin cikin rasa ýaýansu? Ya ce ko akuya ce ake kiwo, idan ta 6ata sai an nemo ta, balle mutum.

Ko me ya sa Shugaba Mohammadu Buhari ya ce ba zai mayar da martani ba sai an samo rahottani daga jihohi?

Ministan ya ce, an kafa Kwamitocin bincike a jihohi 27 na kasar, ba zai yiwu shugaban kasa ya baiyana ra'ayin sa a game da rahoto daya kawai ba. Idan sauran sun kammala ayyukansu, to Gwamnati za ta fito da matsaya.

Da ya ke amsa tambaya akan kiraye kiraye da ake yi na ya ajiye aiki, Lai ya ce ai tun ranar da ya kama aikin Minista ake yi masa wanan kiran, shi kuma bai ajiye aiki ba har yanzu, kuma ba zai ajiye aiki ba.

Lai ya lissafo gi6i 10 a rahoton kwamitin endsars kuma ya dage cewa babu kisa da sojoji suka yi.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00


XS
SM
MD
LG