Kwamitin sulhu na jam'iyyar APC mai mulki ya kaddamar da aikin sulhunta 'yan jam'iyyar bayan takaddamar da ta taso a zaben shugabannin jam'iyyar na jihohi.
Shugaban kwamitin Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci duk masu korafi su rubutawa kwamitin korafin, don daukar matakin da ya dace.
Sai dai manazarta na ganin sai APC ta sake tsarinta, idan tana so ta samu tagoma shi a siyasance.
Shugaban Kwamitin Sulhu na Jamiyyar APC Sanata Abdullahi Adamu wanda ya ke togaciyar 'yan jam'iyya su kaucewa kai kara kotu, ya ce kwamitin zai iya bi diddigi a kowace jiha da irin korafin da a ka gabatar.
Haka nan za su kawo sulhu a iya abin da za su iya yi na nauyin aikin da a ka ba su ga duk abin da zai iya gyaruwa.
Babbar damuwar da ta kunno kai a zaben da APC ta yi a wasu jihohi ita ce, yadda aka samu bangarori biyu da ke ikirarin zama shugabannin jam'iyyar kamar yadda aka gani a jihar Kano.
Misali a Kano, inda kwamitin kasa ya mara baya ga Abdullahi Abbas da gwamna Ganduje ya zaba, bangaren daya shugaban, Ahmadu Haruna Danzago ya ce ba sa ma bukatar kwamitin na Kano, kuma ba za su dauki wani hukunci ba, waje da na helkwatar jam'iyyar na kasa.
Gwamnonin APC irin su Inuwa Yahaya da su ka gudanar da zaben ba tare da samun bangare ba, na ba wa jihohi masu matsala shawarar hanyar mafita da ta hada da aiki da duk masu ruwa da tsaki na jam'iyya.
Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja Dr.Abubakar Umar Kari na shawartar APC ta yi garambawul na tsarin ta fiye da bugewa da salon shugaba Buhari, matukar ta na son ci gaba da tagomashi a siyasance.
Abin dubawa a nan shi ne, yadda babban taron APC zai kaya, alhali a jihohi ma ba a kwashe nikar da waka ba.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda: