Majalisar dattawan ta amince da daidai kasafin da majalisar wakilai ta yi wanda ya kama Naira Triliyan 17.1, sabanin Naira Triliyan 16.3 da shugaba Mohammadu Buhari ya mika wa haddadiyar majalisar a watan Oktoba na bana.
Kasafin ya dauki tsawon lokaci a majalisar dattawa ne domin aiki da suka dukufa yi akan kasafin kudin hukumar zabe, inda a karshe aka amince wa hukumar da kudi har Naira biliyan 305.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, shine shugaban kwamitin kula da hukumar zabe a majalisar dattawa, ya ce a wannan kasafin hukumar zabe ta sami kari, bambancin yadda ake yi a baya saboda a baya ba a bada kudin da hukumar ke bukata kan kari sai dab da zabe amma yanzu an canza lamarin.
Bayanan da Muryar Amurka ta samu game da karin da aki yi akan kasafin kudin na nuni da cewa tun farko an yi kiyasin kasafin akan kudin gangar danyen man fetur dalar Amurka 57 amma a yanzu an daga shi zuwa dalar Amurka 63 wanda ya mayar da kudin zuwa Naira Triliyan 17.1.
Dan majalisar wakilai Abubakar Yahaya Kusada, ya bada hujjar yin karin inda ya ce ana so kasafin kudi ya yi abinda zai tallafawa 'yan kasa kuma ya kasance kowa na da hakki a ciki, shi ya sa sai aka bullo da hanyoyin da zasu samar wa kowacce mazaba wani gurbi a cikin kasafin, wannan shi ya sa aka sami kari a kasafin da bangaren zartarwa suka kawo.
Majalisar ta kwashi shekaru biyu kenan ta na yin kasafin kudin kasar daga watan Janairu zuwa Disamba, sabanin yadda ake yi a baya da ba a ma cika kamalla aiwatar da kasafin a shekara, wani abu da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya danganta da shugabanci mai kyau.
Yanzu dai 'yan kasa sun zuba ido su ga yadda abubuwa za su sauya a kasuwani a daidai lokacin da za a fara aiki da sabon kasafin kudin na shekarar 2022.