Majalisar Dattawan Najeriya, ta amince da saka dokar ta-baci kan hanyoyin gawamnatin tarayya da ke jihar Neja, wadanda suka had arewa da kudancin kasar sbaoda lalacewar da ska yi
Matakin ya biyo bayan wani kudurin gaggawa kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar, wanda ya kawo toshe hanyoyi da nuna rashin amincewa da direbobin tanka suka yi a cikin yan kwanaki da suka gabata.
Mataimakin Mai tsawatar wa a Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudurin inda ya nemi Gwamnatin Tarayya ta yi maza maza ta fitar da wasu makudan kudade har Naira biliyan 300 cikin gaggawa domin a ceto hanyoyin jihar.
Sabi ya ce hanyoyi Gwamnatin Taraiya sun kai tsawon kilomita 32,000 da ‘yan kai kuma dukan su sun lalace matuka.
A cewarsa, akwai wadanda ke shirin rushewa a daidai wannan lokaci musamman gadoji da ke kan hanyoyin.
Daya cikin matafiya da ke yawan bin wadanan hanyoyin idan zai tafi jihohin kudanci kasar kumar direban trela Musa Mohammed ya ce masu motoci kan tafka asarar rayuka da dukiyoyi saboda bacin hanyoyin.
Da yake mayar da martami akan wannan batun, Sanata Sabi Abdullahi ya ce idan ba a yi wadannan ayyuka a cikin gaggawa ba to hanyoyin za su gagara biyu wa, sai an nemi yadda za samar da wasu hanyoyin domin masu safarar neman arziki su samu biyan bukatun yau da kullum.
‘Yan Majalisar Dattawa sun nuna alhininsu da yadda hanyoyin suka lalace matuka tare da yin kira da a gaggauta kai dauki.
Saurari cikakken rahoton Medina Daudadaga Abuja: