Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa Ayuba Waba shi ne ya fadi haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja.
To saidai wasu yan kasa na ganin an gaji da gafara sa.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa Ayuba Waba ya yi barazanar shiga yajin aikin gama gari a fadin kasar sakamakon abinda ya bayana a matsayin karin kudin man fetur da ma wasu abubuwa da Gwamnati ta ce za ta yi a farkon shekara mai zuwa na 2022.
Ayuba Wab ya ce dukan Mambobin Kungiyar ta NLC za su yi watsi da kayaiyakin aiki a fadin kasar na tsawon lokaci amma fa sai bayan kungiyar ta yi tuntuba kafin ta dauki matakin.
Waba ya ce dukan Gwamnatoci idan su ga zabe ya kusa sai su ce za su kara kudin man fetur saboda su hana yan kasa walwala, amma da zabe ya wuce kuma sai a manta da abubuwan da aka yi a baya. Ayuba Wab ya ce Kungiyar Kwadago a shirye ta ke ta bi hakkin maáikata da talakawan kasa a duk lokacinda aka nemi takura masu.
To saidai ga wata Lauya mai zaman kanta Fatima Abubakar, ta ce tana ganin ýan kasa sun fara gajiya da yawan yajin aiki da Kungiyar Kwadago ta ke yi a kasar. Fatima ta ce idan an fara zanga zanga talaka ne yake shan wahala, wasu su mutu, wasu kuma su ji raunuka iri iri, amma a karshe kuma bayan an gana da shugabanin Kungiyar a fadar Gwamnati sai talakawa su ji shiru kuma Gwamnati tana yin abinda ta ke so.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya, domin ba kasafai Kungiyar Kwadago ta ke hana Mahukunta daukan matakai ba, a baya ma an yi haka sai da aka kara kudin man fetur zuwa Naira 162 zuwa 165 wasu sasan kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: