Sanarwar da rundunar sojan kasar ta bayar ta ce harkokin tsaro sun koma daidai a birnin na Kirkuk,
Sai dai har yanzu yankunan dake gabashin yankin Deir el-Zour na hannun 'yan kungiyar ta ISIS.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar sankara ko daji na cigaba da yin barazana ga rayukan bil’adama a fadin duniya, kasashen Afrika cutar ta fi kamari ciki harda Najeriya.
Rundunar ta bayyana haka ne a taron manema labarai da ta saba gudanarwa duk bayan wata uku wanda aka yi a birnin Yola, jihar Adamawa.
Kakakin gwamnatin kasar Kamaru, ministan sadarwar kasar kuma, Isah Ciroma Bakari, ya yiwa manema labarai jawabi a ofishinsa dake birnin Yaoundé akan rikicin dake faruwa a yankin kasar dake magana da harshen ingilishi.
Gwamnan jihar Neja a Najeriya, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kori yawancin kwamishinonin jihar daga kan mukamansu saboda rashin gamsuwa da kamun ludayin yadda suke gudanar da ayyukan cigaban al’ummar jihar.
Nan take Jami'an Myanmar basu maida murtani akan rahoton na Majalissar Dinkin Duniya ba.
'Yan majalissar dokokin Amurka sun kira tashin hankalin da ya faru a garin Charlottesville aikin "ta'addancin cikin gida".
Wannan ne karo na 12 da dakarun suka kai hari ta sama akan kungiyar mayakan dake Somalia.
Kasashen duniya na ci gaba da caccakar Aung San Suu Kyi saboda rikicin dake faruwa a jihar Rakhine.
Bill Gate ya ce matakan da aka dauka akan nasarorin da aka samu na da muhimmanci matuka.
Harin da aka kai ta sama ya auna wasu motoci guda biyu da 'yan bindigar ke ciki akan hanyar Buula-Banin, A yankin Shabelle
Shahid Khaqan Abbasi, wanda aka nada sabon Firamista, ya dade yana zaman Hadimin tsohon Firayin MInistan Pakistan Nawaz Sharif.
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya ce dole ne Rasha ta canza Idan tana So a dage mata takunkumin da aka sanya ma ta.
Shugabannin kungiyoyin adawa na kasar Venezuela na zargin shugaba Maduro da niyyar zama shugaban kama-karya idan har aka yi zaben wakilan da zasu rubuta sabon kundin tsarin mulki da ya ke so.
Wannan dokar zata taimakawa wadanda aka shigo da su Amurka tun suna kanana, basu san wata kasa sai ta Amurka.
Shirin dokar ya ba 'yan majalissar tarayyar Amurka damar kin amincewa da sassauta takunkumin da za a sa akan kasashen.
Tun bayan da kasar Isra'ila ta sanya tsauraran matakan tsaro a wurin Masallacin al-Aqsa, Musulmai a birnin Kudus suka fara nuna bacin ransu ta yin Sallah a wajen Masallacin.
Wasu jami'an gwamnatin Amurka sun ce matakin na zaman wani bangaren kokarin gyara dangantakar dake tsakani Amurka da Rasha.
Kumburin da likitoci suka gano a cikin kwakwalwar Sanata Johan McCain na jam'iyyar Republican na tattare da illa.
Domin Kari