Issa Tchiroma Bakari, Kakakin gwamnatin kasar Kamaru, ya ce kasar ba zata yarda wasu su kawo rarrabuwa a cikinta ba, kuma ba za ta amince da ayyukan ta’addanci ba. A saboda haka gwamnatin kasar ta dauki matakin tura jami’an tsaro a jihohin dake amfani harshen ingilishi guda biyu don tabbatar da tsaro da kare al’ummar yankin.
Rahotanni a baya sun bayyana cewa sojojin kasar sun yi amfani da karfin tuwo har suka kashe wasu fararen hula, amma Tchiroma Bakari ya musanta wannan bayanin. Ya ce sojojin sun dai yi kokarin wargaza wani gungun ‘yan ta’adda dake neman tada zaune tsaye a kasar, da yayi ikirarin cewa daga kasashen ketare suka shigo.
Ya kara da cewa sojojin sun yi nasarar murkushe su. Kodayake akwai wasu masu neman batawa jami’an tsaron suna dake cewa sojojin sun kashe fararen hula sama da dari, wannan zancen ba shi da tushen gaskiya a cewar sa.
Sai dai ministan yada labaran ya ce wasu ‘yan gidan yari a garin Kumbo da suka fito da makamai suna harbe-harbe, jami’an tsaron kasar sun yi amfani da bindigogi akan su har suka kashe ‘yan gidan yarin guda 5 aka kuma tattake wasu.
Tchiroma Bakari ya ja hankalin manema labarai da kungiyoyin agaji na duniya akan su tabbatar da sahihancin labari kafin su yada shi. Ya kara da cewa Majalissar Dinkin Duniya, da kungiyar hadin kan Turai, da kasar Faransa, har ma da kungiyar hadin kan nahiyar Afrika sun yi kira akan kasar ta hau kan teburin neman sasantawa don magance rikicin.
"Shugaban kasar Kamaru Paul Biya na aiki tukuru don ganin ya magance wannna rikicin", cewar Tchiroma Bakari.
Facebook Forum