Hadakar dakarun da Amurka ke jagoranta dake yaki da ‘yan ISIS a kasar Siriya da Iraqi sun ce an ‘yantarda kashi casa’in da biyar cikin dari na birnin Raqqa, kwana daya bayan da 'yan tawayen Syria, da ake kira SDF a takaice suka ayyana samun nasara bayan watannin da aka kwashe ana bata-kashi.
Mai magana da yawun rundunar tsaron taron dangin karkashin jagorancin Amurka, kanal Ryan Dillon, ya ce an cigaba da daukar matakan kakkabewa a yau Laraba a unguwa ta karshe dake birnin.
Wani mai magana da yawun dakarun SDF, da suka kunshi kurdawa da wasu larabawa mayakan sa-kai, ya fada jiya Talata cewa an gama fadan da ake yi a Raqqa, kuma dakarun na SDF na duba sauran mabuyar ‘yan ISIS da kuma nakiyoyin da suka binne a fadin birnin. Ana sa ran ayyana samun nasara a yakin da zarar dakarun suka kammala aikinsu a hukumance.
Facebook Forum