Daya daga cikin shugabannin jama'a a kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, ta soke zuwa babban taron MDD yayin da ta ke fuskantar suka daga kasashen duniya akan yadda ta ke tunkarar tashin hankalin dake faruwa a yammacin Myanmar, wanda ya tilastawa kusan mutane dubu dari uku da saba’in, musulmin kabilar Rohingya arcewa zuwa Bangladesh.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar Zaw Htay ya fada a yau Laraba cewa, Aung San Su Kyi wadda ta taba samun lambar yabo ta Nobel Peace zata kasance a Myanmar don magance zaman fargaban da ake fama da shi a kasar.
Ana yiwa Aung San Suu Kyi kallon zakaran gwajin dafi a fannin dimokradiyya saboda tsare ta da aka yi na tsawon shekaru 10 a karkashin tsohuwar gwamnatin sojan kasar. Amma kuma yadda take nuna halin ko-in-kula gameda kuncin da ‘yan Rohingya a jihar Rakhine ke ciki, da yadda ta yi watsi da rahotannin halin da ake ciki, tana kiran su “rahotannin jabu” da ake yi don daukaka muradan ‘yan ta’adda, ya janyo Allah Wadai daga gwamnatoci da kuma ‘yan rajin kare hakkokin bil’adama, ciki harda wasu daga cikin wadanda suka sami irin lambar da ta samu ta Nobel Peace Laureates.
Facebook Forum