Yayin da ‘yan Boko Haram ke sauya salon hare haren da suke kaiwa a wasu sassan jihohin arewa maso gabashin Najeriya, rundunar sojin saman Najeriya ta lashi takobin kai hare hare a mabuyar ‘yan kungiyar.
Rundunar sojin saman Najeriya ta bada tabbacin cewa za ta cigaba da dakile, tare da kai hare hare a duk sako da mabuyar ‘yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, musamman a wannan lokacin da masu tada kayar bayan ke sauya salon kai hare harensu.
Da yake jawabi a wajen taron manema labaran, kwamandan rundunar sojan Operation Lafiya Dole, Tajuddini Yusuf, ya ce bayan samun nasarar dakile hare haren yan bindigar, rundunar kuma na gudanar da ayyukan jinkai ga al’ummomin da rikicin ya shafa.
Ya kuma ce a wani shirin nuna kwarewa da sanin makamar aiki, da kawo karshen matsalar Boko Haram, rundunar ta bude wani sabon sansani a garin Monguno wanda zai bata damar kai farmaki a sansanonin Boko Haram a arewacin jihar Borno.
Muhammad Idris shine Babban kwamandan rundunar sojan sama dake birnin Maiduguri, wanda ya ce ana samun nasara a yakin da ake yi a garin Maiduguri a yanzu, ya ce sojojin na kokarin kaucewa kai harin da zai iya shafar fararen hula kamar yadda ya faru a baya.
Facebook Forum