Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Daina Baiwa Kungiyoyin 'Yan Tawaye Tallafin Makamai


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Wasu jami'an gwamnatin Amurka sun ce matakin na zaman wani bangaren kokarin gyara dangantakar dake tsakani Amurka da Rasha.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yanke shawarar kawo karshen shirin bada tallafin makamai da horaswa da Hukumar Leken Assiran Amurka ke bayarwa ga kungiyoyin ‘yan tawayen Siriya.

Jami’an Amurka sun ce shugaban ya dauki wannan matakin ne kusan wata daya da ya wuce bayan da ya gana da mai ba shi shawara akan harkokin tsaron kasa, Herbert Raymond McMaster, da shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI Mike Pompeo.

Mai magana da yawun fadar shugaban Amurka ta White house Sarah Huckabee Sanders ba ta ce komai ba akan batun a lokacin da manema labarai suka tambaye ta jiya Laraba.

An fara wannan shirin ne a shekarar 2013 a lokacin gwamnatin tsohon shugaba Barack Obama da zummar karfafa ‘yan tawayen dake fafatawa da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad don kuma hurawa gwamnatin Siriya wuta akan ta yarda a sasanta don kawo karshen yakin basasar da ake yi a kasar.

Tun daga farkon shirin an jefa alamar tambaya akan ko shirin zai yi aiki yadda ya kamata da kuma nuna damuwar kada makaman da Amurka ta ba ‘yan tawayen su kare a hannu ‘yan bangar yake-yake.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG