Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Nuna Rashin Amincewarsa Ga Masu Wariyar Launin Fata


'Yan majalissar dokokin Amurka sun kira tashin hankalin da ya faru a garin Charlottesville aikin "ta'addancin cikin gida".

Majalisar tarayyar Amurka ta zartar da wani kudirin hadin gwiwa wanda ke neman shugaba Donald Trump ya nuna rashin amincewar sa ga kungiyoyin dake nuna kiyayya ga wasu, da masu goyon bayan wariyar launin fata, da tsattsauran ra’ayi, da nuna kyamar yahudawa da kuma turawan dake ganin sun fi kowa a kasar.

Majalissar wakilin kasar ce ta zartar da kudurin jiya Talata, kwana daya bayan da majalissar dattawan kasar ta amince da kudurin. Matakin yanzu ya rage ga Trump, wanda aka caccaka akan murtanin da ya maida game da tashin hankalin da ya faru a lokacin wani gangami da wasu turawa masu kyamar bakar fata a garin Charlottesville dake jihar Virginia suka yi.

Sanata Mark Warner na jam’iyyar Democrat ne ya gabatar da kudurin tare da wasu daga manyan jam’iyyun kasar biyu, Tim Kaine da Richard Blumenthal, su ma daga jam’iyyar Democrat, sai kuma Cory Gardner, da Johnny Isakson da kuma Lisa Murkoski daga jam’iyyar Republican.

Kudurin ya ambachi gangamin da aka yi ranar 11 ga watan Agusta, wanda wasu daruruwan turawa masu fifita jar fata, da ‘yan KKK (suma 'yan rajin kasar jar fata zalla), da kuma ‘yan Neo Nazis (masu kyamar yahudawa) suka yi, suna furta munanan kalaman kiyayya, bayan haka suka kuma yi wata arangama da wasu masu adawa da su

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG