Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mataimakin Shugaban Amurka Pence, Ya Fara Ziyarar Karfafa Gwiwa A Kasashen Turai


Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya ce dole ne Rasha ta canza Idan tana So a dage mata takunkumin da aka sanya ma ta.

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya ce matakan diflomasiyya da Rasha ta dauka don maida martanin sabbin takunkumin da aka sanya mata ba zai hana Amurka ta cigaba da kiyaye matakan tsaronta ba da na kasashen dake kawayenta.

Da yake magana yau Talata a wata ziyara da ya kai kasar Georgia, Pence ya ce sabbin takunkumin da shugaba Donald Trump zai sanyawa hannu ba da dadewa ba, zasu nuna karara cewa, ayyukan da Rasha ke yi a Ukraine da kuma goyon bayan da take yiwa Iran da Siriya, dole ne ta canza matsayarta.

Yawancin ‘yan majalisar tarayya ne suka gabatar da kudurin takunkumin don ladabtar da Rasha akan katsalandan da tayi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar 2016, yayinda kuma suka sanya sabbin takunkumi akan Iran da Koriya Ta arewa. Rasha kuma ta maida martani ta ba Amurka umurnin ta rage yawan ma’aikatanta da suka fi 1,200 a Rasha zuwa 755.


Pence na wadannan ziyarce-ziyarcen ne a kasashen Turai don nuna goyon bayan Amurka ga kasashe kawayenta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG