A Najeriya, matsalar satar jama’a da kuma ‘yan bindiga masu harbin kan mai uwa da wabi na kara ta’azzara a wasu sassan kasar a yayinda babban zabe a kasar ke karatowa.
Shugaba Trump yayi bayani don ya auna shugaban kwamitin Adam Schiff, dan jam'iyyar Democrat, wanda ke yawan sukar shugaban.
Amurka ta yi alkawarin taimakon agajin dala miliyan 20 ga Venezuela, ciki har da abinci da ake bukata sosai da kuma magunguna, amma shugaba Nicolas Maduro ya watsi da taimakon.
Biyo bayan ayyana kan sa a matsayin shugaban rikon kwarya da yayi a makon da ya gabata, Guaido na neman taimakon kasashen duniya, ciki har da majalisar dinkin duniya.
Hukumar zaben INEC ta Najeriya ta gana da shugabannin hadakar kungiyoyin nakasassu, a wani yunkuri na ganin an fadakar da nakasassun sabbin matakan da aka tanadar musu a babban zabe da ke tafe a Najeriya.
A karshen shekarar da ta gabata aka wayi gari da labarin bata da kisan Manjo Janar Alkali, jami'an tsaro sun kama wasu mutane ashirin da hudu da ake zargi da hannu a kisan tsohon hafsan sojan kuma tuni aka gurfanar da su gaban gotu.
Hukumar yaki da cutar SIDA tare da gidauniyar uwar gidan shugaban kasar Niger Hajiya Aissata Isufu da ake kira Guri Vie Meilleur ko Kyakkyawar Rayuwa, sun kaddamar da gwajin cutar sida da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima’i, akan daliban makarantar sakandare.
A ci gaba da neman hanyoyin murkushe matsalar ta’addancin da ya addabi yankin Sahel hukumomi a jamhuriyar Nijer sun kafa wata sabuwar runduna ta musamman da ake kira GARSI mai kunshe da jami’an tsaron jandarma zalla wace za ta yi aiki kafa-da-kafada da wasu takwarorinta na nahiyar Turai.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ake kira INEC a takaice, ta ja kunnen ‘yan siyasa da su kauracewa duk wata dabi’a ta rashin da’a lokacin gudanar da zabe.
“Gwamnatin tarayya ta amince mana, kuma tuni jami’anmu sun yi horo kan yadda za su rika sarrafa makaman, na samu dammar kasancewa daya daga cikin wadanda suka gudanar da wannan horo shekaru biyu da suka gabata.” In ji Sini Kwabe, babban jami’i a hukumar ta FRSC.
Wasu ‘yan jaridar kasar Sudan sun tsunduma cikin yajin aiki, don nuna goyon bayansu ga zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir.
Yau Alhamis ‘yan sanda a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun harba harsasai da barkonon tsohuwa, don wargaza wasu masu zanga-zanga da suka fusata saboda matakin da aka dauka na hana su yin zaben shugaban kasa ranar Lahadi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya koma fadarsa a yau Alhamis bayan da ya kai wata ziyara ta ba-zata ga dakarun Amurka da aka girke a Iraqi.
Sai dai a cewar Rafsanjani, “babbar nasarar da aka samu kan batun yaki da cin hanci da rashawar ita ce, ana ta maganar batun cin hanci da rashawa, saboda haka, wajen wayarwa da mutane kai, an samu nasara” a wannan fannin.
Bayan karin albashin ‘yan sandan Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari yace ya amince da shi, domin tabbatar da tsaro da kuma aiki tukuru, ‘yan Najeriya sun fara maida martani ciki kuwa harda su kansu ‘yan sandan.
Karon farko kenan da mace ta zama shugabar kasar a kasar Habasha. Sahle-Work Zewde ta fara aiki yau a matsayin shugabar kasa bayan ta kwashe shekaru tana aikin jakadancin kasar.
‘Yan sandan birnin New York sun sami wani kunshin sako da basu yarda da abinda ke cikinsa ba a unguwar Manhattan yau Alhamis.
A halin da ake ciki kuma, shugabar hukumar binciken sirrin Amurka ta CIA Gina Haspel ta saurari sautin azabar da aka ganawa Jamal Khashoggi.
Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a jihar Nasarawa sun yi wani zama na musamman da ‘yan takara da suka fafata a zaben fidda gwani don dinke duk wata Baraka da ka iya kunno kai a jam’iyyar.
Da alamu da sauran rina a kaba game da takarar gwamnan jihar Adamawa Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla a inuwar jam’iyar APC wanda kawo yanzu kwamitin gudanarwa na jam’iyyar NWC ya amince da takararsa.
Domin Kari