Masu zanga-zanga da yawa sun kona tayoyi sun kuma lalata cibiyoyin da ake jinyar masu fama da cutar Ebola, a birnin Beni bayan da hukumar zaben Congo ta ce za ta jinkirta zabe har sai watan Maris na badi a Beni, Butembo da garuruwan da ke kewaye, saboda barkewar mummunar cutar Ebola da aka samu a yankin.
Haka kuma hukumar zaben ta jinkirta yin zabe a birnin Yumbi da ke yammacin kasar saboda rikicin kabilancin yankin.
Masu zanga-zangar sun kuma yi tattaki zuwa ofishin zaben Beni, don neman a ba su damar su kada kuri’a ranar Lahadi tare da sauran jama’ar kasar, kuma sun bukaci shugaban hukumar ya yi murabus.
Garuruwan da aka dage zaben akwai masu adawa da Joseph Kabila mai barin gado sosai, shugaban da yake mulkin kasar tun bayan da aka kashe mahaifinsa a shekarar 2001.
Facebook Forum