Kama daga jihar Zamfara da kananan hukumomin Batsari, da Safana dake jihar Katsina, da yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna, da kuma jihar Neja dake arewa maso tsakiyar Najeriya, dubban jama’a ne ke zama cikin yanayin zullumi a sakamakon ta’addancin wadannan ‘yan bindigar.
Alhaji Ma’aru Ma’undu, na daya daga cikin wadanda suka tsallaka rijiya da baya a yankin karamar hukumar Mariga bayan da aka hallaka ‘yan uwansa guda biyu. Ya bayyana cewa suna zaune kawai sai ‘yan bindigar suka zo a guje suka bude masu wuta daga nan suka gudu.
Shugaban karamar hukumar Rafi a jihar Niger, kuma shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya, Alhaji Gambo Tanko, ya tabbatar da cewa suna fuskantar wannan matsalar a yankin amma suna daukar mataki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Niger ta ce tana kokarin fatattakar wadannan miyagun, a ta bakin kakakin rundunar jihar DSP, Abubakar Dan Inna.
Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello, a wani yakin neman zabe da ya je karamar hukumar Rafi mai fama da wannan matsalar, ya ce su na ci gaba da daukar matakai don ganin an sami tsaro a wannan yankin.
Ga karin bayani cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum