Kungiyar wayar da kan jama’a kan harkokin da suka shafi tsarin dokoki da tabbatar da shugabanci na gari, CISLAC, ta ce akwai sauran rina a kaba dangane da yaki da ake yi da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Shugaban kungiyar CISLAC mai hedkwata a Najeriya, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani, ya ce sauya sheka da wasu ‘yan siyasa suke yi, ya haifar da cikas a wannan fanni.
“Cin hanci da ake yi ta bangaren siyasa, saboda yawanci sun canza sheka, sun shiga gwamnati mai ci, saboda haka, za ka ga cewa ba a taba su.” In ji Rafsanjani yayin wata tattaunawa da ya yi da Muryar Amurka ta wayar tarho.
Rafsanjani ya kara da cewa, har yanzu akwai sace-sace da ake samu a bangaren ba da kwangila.
Sai dai a cewar Rafsanjani, “babbar nasarar da aka samu kan batun yaki da cin hanci da rashawar ita ce, ana ta maganar batun cin hanci da rashawa, saboda haka, wajen wayarwa da mutane kai, an samu nasara” a wannan fannin.
Rashin ci gaban kasa, haddasa rigingimu, saka jama'a cikin kuncin rayuwa da haifar da rashin aikin yi, na daga cikin illolin da matsalar cin hanci ke haifarwa ga kasa, a cewar Rafsanjani.
Amma shugaban kungiyar ta CISLAC, ya nuna rashin jin dadinsa kan kalaman da rahotannin suka danganta da shugaba Buhari, wanda suka ruwaito ya ce tsarin dimokradiyya da wasu ‘yan hana ruwa gudu na kawo tarnaki a yakin da ake yi da wannan matsala.
“Gaskiya wannan jawabi ba mu ji dadinsa ba, kamar ya nuna mana ya gaza ne, lokacin da yake kyamfe cewa ya yi zai tabbatar ya ga cewa an yi maganin matsalar cin hanci da rashawa.” In ji Rafsanjani.
Saurari cikakkiyar hirar da Maryam Dauda ta yi da Rafsanjani tare da jin irin matakan da ya kamata a dauka idan ana so a samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya: