Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Nasarawa, Dakta Othman Abdulrahman Ajidagban yayi wannan hudubar ne a yayin da yake zantawa da Muryar Amurka a ofishinsa dake garin Lafia, fadar jihar Nasarawa.
Dakta Abduirahman ya fara da cewa hakkin hukumar zabe ne ta samar da ma’aikata da kayayyakin zabe, ta kuma tabbatarda an fara zabe a kan lokaci an kuma kammala shi a lokacin da aka kayyade.
Shugaban hukumar na jihar Nasarawa yace hakkin hukumar ne ta tattara kuri’u, ta kuma bayyana sakamakon zabe. Ya kara da cewa, ‘yan siyasa ne suka san yadda ake aringizo lokacin zabe, babu hannun hukumar zabe wajen kwace akwatin zabe da ingiza matasa zama ‘yan baranda.
Dakta Abdulrahman ya kuma ja kunnen masu bada kudi don a zabe su akan su kaucewa yin hakan don sauke hakkokin da suka rataya a wuyansu.
Jami’in hukumar zaben ya kuma bukaci hadin kan kowa don gudanar da sahihin zabe a Najeriya.
Ga karin bayani cikin sauti daga Zainab Babaji.
Facebook Forum