Tun da farko sauran ‘yan takarar da suka shiga zaben da suka hada da Dr. Mahmud Halilu Ahmad da akewa lakabi da Modi da kuma Mallam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC, suka yi fatali da zaben fidda gwanin tare da kai kokensu zuwa kwamitin sauraron korafin zabe da jam’iyyar ta kafa.
To sai dai kuma yayin da ‘yan kwamitin ke fatali da korafin da ‘yan takarar suka shigar, yanzu haka wata sabuwa ta kunno inda aka garzaya kotu.
Dr. Mahmud Halilu Ahmad, yace tunda uwar jam’iyyar ta ki ta saurare su, to su sun garzaya kotu domin a soke zaben fidda gwanin.
Amma ko yaya makomar jam’iyyar zata kasance a yanzu a jihar Adamawa ganin irin abinda ke faruwa a yanzu? Wannan ita ce tambayar da aka yiwa wani kusa a jam’iyyar dake bangaren Mallam Nuhu Ribadu, wato Alhaji Usman Ibrahim Jimeta, inda ya ce kowa ya sani cewa tabbas ba ayi zabe ba, amma ya ce har yanzu akwai sauran lokaci kafin zaben shekarar 2019 da za a iya yanke shawara akan abinda zai fi Alheri ga al’ummar jihar Adamawa. Ya kuma ce tabbas shugabannin jam’iyyar APC na kasa sun jefa jam’iyyar cikin halin kaka-na-kayi.
Tuni magoya bayan gwamnan suka soma gudanar da bukukuwa biyo bayan rahotannin cewa kwamitin gudanarwar NWC, ya ba Bindo takarar kujerar gwamna, wanda kuma lokaci ne zai tabbatar da yadda zata kaya tunda yanzu batun na kotu.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum