Bayanai sun yi nuni da cewa, jama’ar da wannan ibtil’in ya shafa sun kwashe kwana uku suna kwana a tituna.
Bayanai sun yi nuni da cewa akalla mutum uku sun rasa rayukansu a jihohin yayin da kusan mutum dubu 500 suke zaune babu wutar lantarki.
Kazalika shirin ya duba martanin da Shugaban Amurka Joe Biden ya mayar bayan da ya samu labarin mutuwar shugaban dakarun haya na kamfanin Wagner, Yevgeny Prigozhin a Rasha.
Ana fargaban shugaban sojojin haya na Wagner Yevgeny Prigozhin ya mutu a wani hatsarin jirgin sama da ya faru a Rasha a ranar Laraba.
Alison-Maduke ta rike mukamin ministar mai a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.
A ranar 25 ga watan Agusta, ake sa ran shugaban Amurka da mukarrabansa 18 za su mika kansu ga hukumomin jihar Georgia da ke Amurka don a tuhume su kan laifukan da ake zargin sun aikata
Fitar da sanarwar ma'aikatun da ministocin za su jagoranta na zuwa ne bayan da majalisar dattawa ta kammala tantance su makonnin da suka gabata.
Ganawar tasu na zuwa ne yayin da ECOWAS ke duba zabin daukan matakin soji a kan masu juyin mulki.
“Ziyarar ta kunshi fitowa karara mu fada musu cewa matakin da suka dauka zai shafi alakarmu da taimakon da muke ba su ta fuskar tattalin arziki, wanda ba mu da zabi illa mu janye su bisa tsarin doka, idan har ba a maido da tsarin dimokradiyya ba.” In ji Nuland.
A cewar Outtara, tura dakarun ECOWAS ba bakon abu ba ne, yana mai cewa, a baya an tura su kasashen Liberia, Saliyo, Gambia da Guinea Bissau.
Wasu kasashe musamman a Afirka, kungiyoyi, malamai da shugabannin gargajiya da jama’a da dama sun nuna a yi taka-tsantsan kan daukar matakin na soji.
“Na farko dai ba mu santa sosai ba, ba mu ma santa ba, to tun da ko ba mu santa ba, ai kun ga ba mu da ma’auni da za mu ce za ta iya wannan aiki ko ba za ta iya wannan aiki ba.” In ji Ganduje.
A ranar Asabar za a bude zagayen da karawa tsakanin Switzerland da Spain, sai karawa ta biyu tsakanin Japan da Norway.
Sannan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a gaban wata kotu a Washington D.C., inda aka tuhume shi da laifin yunkurin sauya sakamakon zaben 2020.
A ranar Laraba, Tinubu ya aike da jerin sunaye 19 a karo na biyu, ciki har da sunan Shetty.
“Ina kira ga Amurka da daukacin kasashen duniya, su taimaka wajen maido da doka da oda a Nijar." Bazoum ya ce cikin makalar da ya rubuta.
Janar Abdulsalami Abubakar ya ce tawagar za ta je Nijar ta gana da shugabannin da suka yi juyin mulki su kuma mika musu bukatun kungiyar Kungiyar ECOWAS.
A tsakiyar watan Yulin da ya gabata tsohon shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa.
Gangamin har ila yau na zuwa ne yayin da kasar ta Nijar take cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga Faransa.
Domin Kari