Adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar girgizar kasar da ta auku a Morocco ya kai 2,100 a cewar kamfanin Dillancin Labarai na AP.
A ranar Juma’a girgizar kasar mai karfin maki 6.8 takwas ta afkawa yankin Marrakech da wasu lardunan kasar biyar.
Tafiyar sa’a uku da rabi ne a mota tsakanin Marrakech da Casablanca - birni mafi girma a kasar ta Morocco.
Bayanai sun yi nuni da cewa, jama’ar da wannan ibtil’in ya shafa sun kwashe kwana uku suna kwana a tituna.
Sojoji da kungiyoyin agaji na kasa da kasa na ta dunguma zuwa yankin da girgizar ta auku cikin manyan motoci da jirage masu saukar ungulu a cewar AP.
Sai dai yayin da kasashen duniya ke ta tayin kai dauki, hukumomin kasar ta Morocco sun ce daga kasashen hudu kacal za su karbi taimako.
Kasashen sun hada da Sifaniya, Qatar, Birtaniya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutum dubu 300 girgizar kasar ta shafa.
Dandalin Mu Tattauna