Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Ba Ni Na Iya Ne Suka Ba Da Sunan Maryam Shetty, Mu Ba Mu Ma Santa Ba – Ganduje


Maryam Shetty da Ganduje (Hoto: Faecebook/Maryam Shetty)
Maryam Shetty da Ganduje (Hoto: Faecebook/Maryam Shetty)

“Na farko dai ba mu santa sosai ba, ba mu ma santa ba, to tun da ko ba mu santa ba, ai kun ga ba mu da ma’auni da za mu ce za ta iya wannan aiki ko ba za ta iya wannan aiki ba.” In ji Ganduje.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, ‘yan ba-ni-na-iya da ke fadar shugaban kasa ne suka ba da sunan Maryam Shettima wacce aka fi sani da Maryam Shetty.

A ranar Larabar da ta gabata Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya mika sunan Shetty cikin karin sunaye 19 da ya aikawa Majalisar Dattawa don ba su mukamin minista daga Kano.

Kasa da sa’a 48 da ba da sunan, Tinubu ya cire sunan Shetty daga ministocin ya sauya da na Dr. Mariya Mahmud Bunkure.

Wannan lamari ya janyo ka-ce-na-ce musamman a kafafen sada zumunta, inda aka yi ta laluben abin da ya faru aka cire sunan Shetty wacce matashiya ce.

Sai dai yayin wata hira da ya yi da kafafen yada labarai a ranar Asabar ciki har da gidan Freedom Radio na Kano, tsohon gwamnan Kano Ganduje ya zargi wasu a fadar shugaban kasar da yin riga malam masallaci.

Dr. Maryam Shetty (Hoto: Facebook/Maryam Shetty)
Dr. Maryam Shetty (Hoto: Facebook/Maryam Shetty)

“Ka san a fada, a ko da yaushe, akwai ‘yan ba-ni-na-iya, saboda wannan suna sai kawai muka gan shi daga sama.

“Na farko dai ba mu santa sosai ba, ba mu ma santa ba, to tun da ko ba mu santa ba, ai kun ga ba mu da ma’auni da za mu ce za ta iya wannan aiki ko ba za ta iya wannan aiki ba.” In ji Ganduje.

A cewar Ganduje, duba da cewa shugaban kasa yana da hurumi da ikon ya nada wanda yake so, hakan ya sa ba su kalubalanci zabin Shetty ba.

Sai dai shugaban na jam’iyyar APC, ya zayyana wata matsala da ta janyo Shetty ta rasa kujerar ministan.

“Inda gizon yake saka, shi ne batun soshiyalmidiya. Kana zato ka yi abu ba wanda ya sani, sai ka ga kowa ma ashe ya sani. Watakila ma kai da ka yi abin ma an fi ka sanin ka yi.” Ganduje ya ce.

Ya kara da cewa, “soshiyalmidiya suka fara fitowa suna cewa wannan mai ta lakanta da za ta iya wannan mulki, kuma yanzu mutanen Kano, har ma ta kai irin wannan ce za ta wakilci mutanen Kano. To wannan sai ya kawo damuwa, kun ga damuwar nan ba da Ganduje ta zo ba, ba daga sauran jama’a ta zo ba, amma damuwa ta zo daga al’uma wadanda ke da hange.

Dr. Mariya Mahmud Bunkure (Hoto: Facebook/ Dr. Mariya Mahmud Bunkure)
Dr. Mariya Mahmud Bunkure (Hoto: Facebook/ Dr. Mariya Mahmud Bunkure)

A cewar Ganduje, Tinubu ya tambaye shi ko akwai bukatar a canja sunan Shetty saboda tsokaci da aka ta yi a kafafen sada zumunta a kanta ya kai ga kunensa “na ce kwarai da gaske kuwa, domin mulki irin wannan na farko yana bukatar dattaku, na biyu yana bukatar sani, ba bundun-bundun ba, ba awun igaya ba. Na uku wacce rawa ka taka a wajen tsayar da wannan gwamnati a siyasance.”

Ganduje ya ce ya fadawa Tinubu cewa ba shi ya ba da sunan Shetty ba kuma bai san wanda ya mika sunanta ba.

An dai yi ta ce-ce-ku-ce a fili da kafafen sada zumunta bayan da aka cire sunan Shetty aka maye da na Dr. Mariya wacce tsohuwar kwamishinar ilimi mai zurfi ce a wa’adin mulkin Ganduje na biyu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG