Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rabawa ministoci 46 mukamai bayan da majalisar dattawa ta kammala tantance su a kwanakin baya.
Tinubu ya nada tsohon Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike a matsayin Ministan Babban birnin Tarayya na Abuja.
Kazalika Tinubu ya nada Festus Keyamo a matsayin Ministan sufurin sama.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru ne zai jagoranci ma'aikatar tsaro a cewar kafafen yada labaran Najeriya.
Ga sauran jerin ministocin da Tinubu ya rabawa mukamai:
Ministar raya al’adu da Ggrgajiya – Hannatu Musawa
Karamin Ministan Tsaro – Bello Matawalle
Karamin Ministan Ilimi – Yusuf T. Sunumu
Ministan Gidaje da raya Alkarya – Ahmed Dangiwa
Karamin Ministan Gidaje da raya Alkarya – Abdullahi Gwarzo
Ministan Kasafin kudi da Tsara Tattalin Arziki – Atiku Bagudu
Karamar Ministan Birnin Tarayya – Mariya Mairiga Mahmud
Karamin Ministan kula da albarkatun kasa da na ruwa da tsaftace muhalli – Bello Goronyo
Ministan Noma da Samar da abinci – Abubakar Kyari
Ministan Ilimi - Tahi Momoh
Ministan Cikin gida – Sa’idu Alkali
Ministan harkokin wajen – Yusuf Tuggar
Ministan Tsara harkokin lafiya da al’amuran ci gaba – Ali Pate
Ministan Hukumar ‘yan sanda – Ibrahim Geidam
Karamin Ministan Bunkasa harkokin Karafa – U. Maigari Ahmadu.
Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani – Bosun Tuani
Karamin Ministan muhalli – Ishak Salako
Ministan Kudi da shirya tsare-tsare tattalin arziki – Wale Edun
Ministan kula da teku da albarkantu – Bunmi Tunji-Ojo
Ministan kula da wutar lantarki – Adebayo Adelabu
Karamin Ministan lafiya da kula da walwala – Tunji Alausa
Ministan kula da albarkatun kasa – Dele Alake
Ministan kula da fannin yawon bude ido – Lola Ade-John
Ministan Sufuri – Adegboyega Oyetola
Ministar kula da ma’akatu, kasuwanci da saka hannun jari – Doris Anite
Ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha – Uche Nnaji
Karamin Ministan kwdago da daukan ma’aikata – Nkiruka Onyejeocha
Ministar Mata – Uju Kennedy
Ministan Ayyuka – David Umahi
Ministan Matasa – Abubakar Momoh
Ministar ayyukan jin-kai da yaki da talauci – Betta Edu
Karamin Ministan albarkatun Gas – Ekperipe Ekpo
Karamar Ministar Albarkatun mai – Heineken Lokpobiri
Ministan Wasanni – John Enoh
Karamin Ministan noma - Aliyu Sabi Abdullahi
Dandalin Mu Tattauna