Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tura wata tawaga zuwa Jamhuriyar Nijar a wani mataki na shawo kan rikicin juyin mulki da kasar ta fada ciki.
Tawagar ta tafi Nijar ne karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa na mulkin soji Janar Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III.
Cikin tawagar har ila yau akwai Shugaban gudanarwar kungiyar ECOWAS Omar Alieu Touray a cewar wata sanarwa da kakakin Tinubu Ajuri Ngelale ya fitar.
“Tawagar ta tashi daga Abuja a ranar Alhamis zuwa Yamai bayan kammala wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa.” Sanarwar ta ce.
Janar Abdulsalami Abubakar ya ce tawagar za ta je Nijar ta gana da shugabannin da suka yi juyin mulki su kuma mika musu bukatun kungiyar Kungiyar ECOWAS.
Sanarwar ta kara da cewa, an tashi wata tawaga ta daban karkashin Ambasada Babagana Kingibe zuwa Libya da Algeriya duk a kokarin da ake yi na shawo kan rikicin na Nijar.
Hakan na faruwa ne yayin da manyan hafsoshin sojin kasashen kungiyar ECOWAS ke shirin kammala wani taro da suke yi a Abuja kan rikicin na Nijar.
A ranar 26 ga watan Yuli, sojojin da ke gadin fadar Shugaba Mohamed Bazoum suka tsare shi tare da ayyana juyin mulki.
Dandalin Mu Tattauna