Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Birtaniya Ta Tuhumi Diezani Kan Zargin Karbar Cin Hanci


Tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Maduke
Tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Maduke

Alison-Maduke ta rike mukamin ministar mai a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.

Wata kotu a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar shugabar kungiyar kasashe masu arzikin mai ta OPEC, Diezani Alison-Madueke da laifin karbar cin hanci a lokacin tana rike da mukamin ministar mai a Najeriya.

Hukumar da ke yaki da manyan laifuka ta NCA a Birtaniya ce ta bayyana hakan a ranar Talata.

“Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da kujerarta a Najeriya ta karbi kyautar kudade saboda ta ba da wasu kwantiragi na miliyoyin fam,” In ji Andy Kelly da ke shugabantar sashen laifukan kasa da kasa a hukumar ta NCA.

An ba da belin Alison-Madueke mai shekaru 63 tun bayan da aka kama ta a watan Oktoba a London a shekarar 2015.

A ranar 2 ga watan Oktoba ake sa ran za ta gurfana a gaban kotu a cewar NCA.

Lauyan tsohuwar ministar man ya fadawa AFP cewa Alison-Madueke za ta kalubalanci zarge-zargen da ake mata.

Alison-Madueke ta rike mukamin ministar mai a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.

Ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin ministar mai a Najeriya da mukamin shugabar kungiyar ta OPEC.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG