Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juyin Mulki: Blinken Ya Gana Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadu Issouhou


Tsohon Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou
Tsohon Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou

Ganawar tasu na zuwa ne yayin da ECOWAS ke duba zabin daukan matakin soji a kan masu juyin mulki.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya gana da tsohon shugaban Nijar Mohamadu Issouhou inda ya bayyana masa damuwarsa kan yadda ake ci gaba da tsare da Shugaba Mohamadu Bazoum da iyalansa.

Wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya fitar, ta ce, Blinken ya nuna wa Issouhou takaicinsa kan yadda sojojin da suka yi juyin mulki suka ki sakin Bazoum duk da magiyar da ake ta yi daga sassan duniya.

Sakatare Blinken kamar yadda sanarwar ta nuna, ya bayyanawa tsohon shugaban na Nijar kudurin Amurka na ci gaba da neman hanyar da za a sasanta wannan rikicin shugabanci ta hanyar Lumana – yana mai cewa Amurka a ko da yaushe na cikin shirin ci gaba da zama babbar kawa ga Nijar don ci gaban kasar da yankin Sahel.

A ranar 26 ga watan Yuli dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar karkashin jagorancin Janara Abdourahamane Tchiani, suka kifar da gwamnaton Bazoum suka kuma tsare shi da iyalansa da wasu jami’an gwamnatinsa.

Kungiyar ECOWAS da sauran kungiyoyi da kasashen duniya da dama, sun yi Allah wadai da wannan juyin mulki tare da yin kira da a saki Bazoum.

A ranar Alhamis kungiyar ta ECOWAS ta yi wani zama na biyu a Abuja, babban birnin Najeriya inda ta cimma matsayar daukan matakin soji akan kasar ta Nijar muddin ba a maido da kaaar bisa tsarin dimokradiyya ba.

A baya, dakarun na Nijar sun take wani wa’adin mako guda da kungiyar ta ECOWAS ta gindaya musu kan wannan kira da ta yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG