Ranar Talata 27 ga watan Agusta na shekarar 1991 gwamnatin mulkin soji a Najeriya ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sanar da kirkiro karin jihohi 9 a kasar, kuma jihar Jigawa na daga cikinsu.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasar a zaben bana na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya fara gudanar da taron gangaminsa na neman kuri’a a Kano.
Dinbin sarakunan gargajiya, malamai da kusoshin gwamnati daga sassan Arewacin Najeriya na cikin dubun dubatar al'umar Musulmi ne suka halarci Sallar jana'izar mai martaba sarkin Dutse, Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi wanda Allah ya yiwa rasuwa a jiya Talata.a babban asibitin kasa dake Abuja.
Shugaban Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki jihar Kano, tare da ya bude tashar fiton kayayyaki ta nesa da teku da kuma sabuwar tashar samar da lantarki mai amfani da albarkatun ruwa da gwamnatin Kano ta gina.
Dattawa da kwararru a fannoni dabam daban na rayuwar bil’adama daga jihohin Kano da Jigawa a Najeriya sun ce lokaci yayi da al’umma da mahukunta a jihohin biyu zasu kalli alkibila guda domin magance kalubalen da ke barazana ga makomar rayuwarsu.
Yayin da rashin sanin tabbas ya harzuka mafi yawan yan Najeriya game sabbin takardun da har yanzu basu kai ga hannun yan kasar ba, kwararru sun shawarci babban bankin Najeriya.
An haifi Mohammed Rabiu Musa da akafi sani da Rabiu Musa Kwankwaso shekaru 67 da suka shude a garin Kwankwaso na karamar hukumar Madobi a jihar Kano Najeriya.
Kalaman na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan takarar gwamna a jihar Kano suka sanya hannu akan yarjejeniyar mutunta juna da kiyaye doka da oda yayin kamfe.
Kungiyoyin mata a Najeriya na kara kaimi wajen wayar da kan ‘yan uwan su a birnin da karkara game da muhimmancin shiga adama da su a harkokin zaben kasar, domin samar da gwamnatin da zata kula da bukatun su.
An yi kira ga 'yan takarar da su rika sanya ido akan wadanda suka nada a mukamai domin su tabbatar da cewa sun rike amana.
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta na ci gaba da aikin tantance mutanen da annobar ambaliyar ruwa ta shafa a jihar domin basu tallafin daya kamata da nufin rage radadin rayuwa da suke ciki.
Mutanen da ambaliyar ruwa ta lalata musu gonaki da gidaje a jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da korafi kan yadda hukumomin jihar da-ma na tarayya suka yi watsi da makomar su.
Baya ga farfaganda, dukkanin jami’iyyun sun bullo da tsarin ganawa ta musamman ga muhimman rukunan jama’a, wa lau a shiyya ko jiha.
Gabanin gudanar da gangamin neman kuri’a a jihar Kano yau Laraba, a jiya Talata dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyoyin malaman musulmi na yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Domin Kari