Gabanin gudanar da gangamin neman kuri’a a jihar Kano yau Laraba, a jiya Talata dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya gana da kungiyoyin malaman musulmi na yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumar dake yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA, ta ce shigar mata, musamman masu aure cikin harkokin shaye-shaye na daga cikin manyan kalubale da take fuskanta wajen gudanar da ayyukanta a jihar Kano.
Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya tace yawan sauya wa alkalai wuraren aiki da Odar da alkalan kan bayar barkatai a yayin shari’u, na daga cikin kalubalen da take fuskanta wajen gudanar da ayyukanta.
Kungiyoyin kula da harkokin addinin Musulinci na ci gaba da bayyana matsayar su dangane da hukuncin babbar kotun shari’ar Musulicin ta Kano game da shari’ar da ka yi wa Malam Abduljabbar Nasiru Kabara.
An kammala taron bita da kara wa juna sani na yini uku a Kano ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an hukumomin Hisbah na jihohi 6 a arewa maso yammacin Najeriya.
An fara taron bita da karawa juna sani na yini uku a Kano, ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an Hisbah na jihohi 6 dake arewa maso yammacin Najeriya da nufin neman dabaru da hikimar tunkarar kalubalen zamantakewar gida da cin zarafin mata da kananan yara.
A wani mataki na dakile akidar yanayin siyasa, kwamitin tabbatar da zaman lafiya na jihar Kano da hadin gwiwa da hukumar NBC sun gudanar da taro na musamman da shugabannin kafofin labaru da kuma wakilan manyan kafofin labarai na cikin gida da na ketare wadanda ke aikin tura rahotannin daga Kano.
Kwamiti wadda ke karkashin jagorancin farfesa Ibrahim Umar ya bayyana damuwa da kakkausan harshe game da yadda wasu daga cikin shugabanin siyasa a Kano ke kokarin dumama yanayi a jihar ta hanyar furta kazaman kalamai da ka iya tunzura magoya baya
Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya, S.O.N , tace yanzu haka Najeriyar na kokarin cika sharrudan samun rijistar shiga jerin kasashen duniya da ake damawa da su a hada-hadar cinikayayyar kayayyaki bisa manufa da tsarin kasuwanci na Halal.
Kungiyoyin rajin shugabanci na gari a jihar Kano sun yi Allah wadai da kalaman tunzura Jama’a na baya-bayan nan da suka fito daga bakunan shugabannin Jam’iyyun APC da NNPP na jihar ta Kano.
Jama'a da dama a kudu da arewacin Najeriya sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da asarar dukiyoyi.
Yau Alhamis aka shiga rana ta biyu da fara sauraron shiri’ar mutumin kasar China nan Mr Frank Geng Quatrong wanda ake tuhuma da kisan gilla ga Ummukulsum Sani Buhari a Kano a ranar 16 ga watan satumba.
Al’umar wadannan yankuna sun ce za su yi amfani da katunansu na zabe wajen neman mafita, suna masu cewa, duk dan siyasar da ya zo neman kuri’unsu, sai ya musu alkawarin sama musu ababen more rayuwa kafin su zabe shi.
Domin Kari