Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Najeriya Zai Yi Tasiri A Afirka Idan Aka Gudanar Da Shi Cikin Lumana - MDD


'Yan takarar gwamna a jihar Kano
'Yan takarar gwamna a jihar Kano

Kalaman na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan takarar gwamna a jihar Kano suka sanya hannu akan yarjejeniyar mutunta juna da kiyaye doka da oda yayin kamfe.  

Yayin da makonni kalilan suka rage a gudanar da babban zabe a Najeriya, majalisar dinkin duniya ta baiwa hukumomin kasar tabbatacin goyon baya domin samun sahihin zabe da sakamakon sa zai karbu ga kowa.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ‘yan takarar gwamna a jihar Kano suka sanya hannu akan yarjejeniyar mutunta juna da kiyaye doka da oda yayin kamfe.

A jawabinta a wurin rantsuwar kiyaye doka da oda da ‘yan takarar gwamnan Kano na Jam’iyyu daban daban wadda ya gudana a birnin Kano, Madam Giovanie Biha, wakiliya ta musamman ga sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yankin Sahel, ta ce gudanar da zabe cikin lumana a Najeriya na aika sahihi kuma muhimmin sako ga nahiyar Afrika da sauran sassan duniya.

Ta kara da cewa, yayin da take aiki tare da kwamitin zaman lafiya na Janar Abdussalami Abubakar da hukumar kula da ayyukan kungiyar ECOWAS ta kasashen nahiyar Afrika ta yamma da kuma kungiyar tarayyar Afrika, maijalisar dinkin duniya ta baiwa hukumomin Najeriya tabbacin goyon bayan ta wajen tsarawa da gudanar da sahihin zabe da zai karbu ga kowa da kowa.

Wajen taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin yakin neman zabe a Kano
Wajen taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya yayin yakin neman zabe a Kano

Malam Garba Lawan da ke zaman sakataren ofishin Kano na hukumar zabe ta Najeriya INEC wanda ya wakilci kwamishin zabe na Kano a wurin taron, ya ce za su ci gaba da kokarin tabbatar da zabe na gaskiya bisa tanadin ka’idojin hukumar da dokokin kasa.

Ayoyi 12 ne kundin yarjejeniyar ya kunsa, kuma aka karanta musu suka ji gabanin su rattaba hannu da ke tattabar da amincewar su.

Ayoyin yarjejeniyar sun hada da cewa, “Na amince tare da yin alkawarin cewa zan tallafawa hukumomin gwamnati, musamman hukumar zabe da jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan sun a dakile duk wanin yunkuri da zai kawo cikas ga zaman lafiya a Kano a yayin zabe ko bayan fitar da sakamakon zabe”.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa kakakin rundunar ‘yan sandan Kano yace hukumar ‘yan sanda ba zata saurarawa duk wani dan takara ko magoya baya ba da suka ki mutunta kunshin yarjejeniyar.

Allon taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya a zaben Kano
Allon taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya a zaben Kano

Rev. Father Attah Barkindo, daya wakilci shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa yace zasu saka ido sosai akan ‘yan siyasa, domin bibiyar kalaman da suke furtawa a yayin da suke rangadin neman kuri’ar ‘yan kasa.

Ya ce muddin suka ji dantakar da kalaman da suka ci karo da sharrudan yarjejeniyar, babu shakka za su ci hankalin sa, domin kuwa kundin yarjejeniyar ka iya zama hujja akan sa lokacin da aka samu tarzoma sanadin sa ko magoya bayan sa.

Ya zuwa yanzu dai wannan kwamitin zaman lafiya da tsohon shugaban Najeriya Janar Abdussalami Abubakar ke shugabanta ya jagoranci rattaba hannu akan yarjejeniya a tsakanin ‘yan takarar gwamnan a 15 daga cikin jihohin kasar talatin da shida.

XS
SM
MD
LG