A yayin taron kolin da kungiyar kwararru a fannoni dabam daban mai suna Kano LEADS ta shirya, makomar muhalli, ilimi, tattalin arziki, zamantakewa, kiwon lafiya, hadin kan jama’a da karfafa tsaro a tsakanin al’ummar jihohin Kano da Jigawa, na cikin manyan batutuwan da aka yi bitarsu da kuma tattauna rawar da mutune da kungiyoyi zasu taka, kana da yadda ya kamata hukumomi su tunkari lamuran.
Wazirin Dutse, tsohon Ministan lantarki na tarayyar Najeriya, Alhaji Bashir Dalhatu, na daya daga cikin manyan bakin da suka halarci taron, ya ce duk abin da ya shafi Kano tamkar ya shafi Jigawa, haka kuma al’amarin da ya shafi al’umomin wadannan jihohi guda biyu tamkar ya shafi duk dan arewacin Najeriya ne. A saboda haka, ya kamata shugabanni su kiyaye su daina yi wa mutane alkawuran da ba zasu iya cikawa ba.
Alhaji Abubakar Sadiq Umar, da ke zaman sakatare Janar na kungiyar ta Kano LEADS, ya ce babban abin da kungiyar ta sanya a gaba shi ne zaburar da mutane, domin kowa ya tashi tsaye ya taka rawar da ta kamata domin al’amuran rayuwa su daidaita.
Shehunnan malamai da kwararru sun gabatar da makala a bangarori dabam daban, inda mukalar Farfesa Aliyu Salisu Barau na tsangayar nazarin harkokin kimiyyar muhalli a jami’ar Bayero Kano ta mayar da hankali kan kalubalen gurbatar yanayi da sauyinsa.”
"Yanzu halin da Kano ke ciki shi ne yanayin iskar da ke kadawa a birnin ta gurbata fiye da manyan birane da ke da masana’antu, ba ma a nahiyar Afrika kadai ba har ma a Turai, sannan yanayin zafi ya karu a birnin Kano saboda cunkoso. Haka kuma wurare masu dausayi da ruwa, da kudaddufai duk an cike su,” a cewar Farfesa Barau.
Wannan batu ya sanya Alhaji Bashir Dalhatu ke cewa akwai bukatar gwamnatocin Kano da Jigawa su rinka samar da manufofi na bai daya da zasu zama alkibilar shugabannin gwamnati kan al’amuran da zasu ciyar da rayuwar al’umma gaba babu katsewa.
Kungiyar Inuwar Jama’ar Kano ta su marigayi Alhaji Magaji Danbatta, da Gidauniyar Kano wadda su Alhaji Aminu Dantata suka assasa a shekarun baya, na cikin kungiyoyin da suka yi yunkurin tabbatar da cewa tsohuwar jihar Kano ta ci gaba da rike kanbinta a fagen siyasa, ilimi, tattalin arziki da kuma zamantakewar al’umma.
Saurari rahoton cikin sauti: