Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shawarar Kwararru Kan Yadda CBN Zai Magance Matsalar Da Ake Fuskanta A Najeriya


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Mataimakinsa tare da gwamnan babban bankin Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Mataimakinsa tare da gwamnan babban bankin Najeriya.

Yayin da rashin sanin tabbas ya harzuka mafi yawan yan Najeriya game sabbin takardun da har yanzu basu kai ga hannun yan kasar ba, kwararru sun shawarci babban bankin Najeriya.

Kwararru akan harkokin bankin da hada-dahadar kudade a Najeriya, sun shawarci babban bankin kasar ya kara kaimi wajen daukar matakan wayar da kai, bisa manufa da burin da ake muradin cimmawa game da batun sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudade na kasar.

Sunce akwai bukatar bankin na CBN ya sassauta sharrudan da bankunan kasuwanci ke gindayawa kafin bude asusun ajiya ga ‘yan kasa.

Malam Aliyu Wada Nas, shugaban cibiyar kwararru harkokin banki ta Najeriya, wato (Chartered Institute of Bankers of Nigeria, CIBN) ya ce saukaka sharrudan zai karfafawa ‘yan kasa gwiwa su rinka bude asusun ajiya a bankuna, la’akari da cewa, sabuwar manufar babban bankin kasa ta takaita amfani da mu’amala takardun kudi a hannun Jama’a, tare da komawa mu’amula da mafi yawan kudaden ta yanar gizo.

A zantawa da wakilin sashin Hausa a Kano, Malam Aliyu Wada Nas, ya yi bayanin cewa, “Ya kamata babban bankin kasa CBN ya baiwa wakilan bankin (wato masu POS) damar budewa Jama’a asusun ajiya a bankuna, domin hakan zai taimaka wajen ganin cewa, mutane da dama sun sami sukunin mayar mu’amalar su ta banki”

Dangane da kalubalen da ake fuskanta na karancin sabbin takardun kudi kuwa, Malam Aliyu Wada Nas ya yi hasashen cewa, tilas ne Jama’a su kara hakuri, domin yanayin ka iya kaiwa wani lokaci kafin al’amura su dai-daita.

Ya zuwa jiya Juma’a, reshen Kano na babban bankin Najeriya ya ce ya saki kimanin naira biliyan 12 na sabbin takardun kudade ga bankunan kasuwanci dake aiki a fadin jihar, inji Konturollan bankin Alhaji Umar Ibrahim Biu.

Ya ce mahukuntan bankin bisa jagorancin Daraktar kula da harkokin fasahar sadarwa a shalkwatar su dake Abuja, Hajiya Rakiya Mohammed, sun bullo da dabaru daban daban domin ganin cewa, sabbin takardun kudaden sun kewaya sassan jihar.

Mahukuntan bankin na CBN a Kano sun roki shugabannin kungiyar Miyetti Allah a jihar su taimaka wajen wayar da kan Fulani game da wannan tsari, a cewar Hajiya A’ishatu Mohammed Abubakar, shugabar bangaren mata ta kungiyar a Matakin kasa baki daya.

Shi-ma Darakta Janar na kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kano, Abdullahi Bakoji Adamu, ya ce bankin na CBN ya yi alkawarin samar da adadi mai yawa na sabbin takardun kudaden domin bada canji ga mambobin kungiyar dake yankunan karkara.

Abin jira dai a gani shine, ko matakan da babban bankin Najeriyar ke dauka zasu magance matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta biyo bayan sauya fasalin takardun kudin kasar na Naira dubu daya da naira dari biyar da kuma naira dari biyu, a dai-dai lokacin da wa’adin karbar tsaffin takardun ke karewa a ranar talata mai zuwa.

XS
SM
MD
LG