Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JIGAWA: An Tara Naira Biliyan 1 Don Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa


Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, arewacin Najeriya
Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, arewacin Najeriya

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta na ci gaba da aikin tantance mutanen da annobar ambaliyar ruwa ta shafa a jihar domin basu tallafin daya kamata da nufin rage radadin rayuwa da suke ciki.

A zantawa da wakilin sashin Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, gwamnan jihar Badaru Abubakar yace ya zuwa yanzu kwamitin da gwamnati ta kafa domin neman gudunmawa ya tattara fiye da naira biliyan guda daga hukumomi kungiyoyi da dedekun mutane, baya ga kason gudunmawa na gwamnatin jihar.

Gwamnan yace “kwamitoci guda biyu da gwamnati ta kafa bayan ambaliyar sun hada dana tantance mizanin asarar da mutane sukayi da kuma yanayin wahala da suke ciki sanadiyyar ambaliyar kuma aka danka masa alhakin lalubo tallafi daga gwamnatoci, hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu. Kwamiti na biyu, a cewar gwamna Badaru shine, na gano musabbabin ambaliyar da nufin daukar matakan kariya da suka dace”.

Gwamnan ya ce yanzu haka kwamitin neman gudunmawa ya samo naira biliyan dad a dubu dari biyu kuma ana ci gaba da aikin tantance mutanen da suka cancanci cin gajiyar tallafi.

Dangane da hanyoyin mota da gadojin da ambaliyar ruwan ta lalata kuwa, gwamnan na jihar jigawa ya yi bayanin cewa, bayan aikin tantance gadojin da hanyoyin, gwamnati ta kiyasata kashe fiye da naira biliyan shida domin gyara su kafin zuwan damina ta gaba.

Da aka tambayi gwamna game da makomar manufofi da tsare-tsaren gwamnatin sa bayan ya bar mulki, gwamna Badaru Abubakar yace yana day akinin cewa, magajin sa zai ci gaba da abubuwan daya fara la’akari da cewa, a Jigawa sun kafa tarihi, domin shi-ma duk da banbancin Jam’iyya, said a yayi kokarin kammala ayyukan da gwamnatin daya gada ta fara, saboda kare dukiyar al’umar Jigawa daga asarar kudaden da aka kashe wajen fara ayyukan baya.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG