Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Amfani Da Dabarar “Farfaganda” Na Tasiri A Siyasar Najeriya?


'Yan Najeriya a wajen gangamin siyasa
'Yan Najeriya a wajen gangamin siyasa

Baya ga farfaganda, dukkanin jami’iyyun sun bullo da tsarin ganawa ta musamman ga muhimman rukunan jama’a, wa lau a shiyya ko jiha.

Yayin da dan takarar shugaban Najeriya karkashin Jam’iyya mai Mulki, APC ya karkare gangamin neman kuri’a a jihar Kano, masu kula da lamura da masana dimokradiyya a kasar na ci gaba da yin fashin baki akan kalaman neman goyon baya ta sigar farfaganda da kuma alkawuran da manyan ‘yan takara ke yi wa ‘yan Najerijeriyar.

A yayin gangamin zabe a Kano, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya yi kalaman da har-ma wasu ke fassarawa a matsayin shagube irin na siyasa ga abokin hamayyarsa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

“Idan aka tambayeshi ta yaya ka tara arziki sai ya kan ce shi-fa ta hanyar hada-hadar sufuri da sauran al’amuran kasuwanci ne ya samu kudinsa, amma ya manta cewa, a tsarin aikin gwamnati, idan kai jami’in kwastam ne sana’ar noma kawai dokar kasa ta amince ka yi lokacin da kake bakin aiki, kenan anan wane ne yake rudar wa?”

Su ma dai nasu bangaren, a yayin taruka da gangaminsu na neman kuri’a, Jam’iyyar PDP da kwamitin tallata dan takarar ta Atiku Abubakar na danganta rashin koshin lafiya ga Bola Tinubu na APC da kuma wata tuhuma da aka ce wata kotu a Amurka na yi masa, domin su nuna nakasunsa ga ‘yan Najeriya.

Atiku Abubakar a waje gangamin siyasa
Atiku Abubakar a waje gangamin siyasa

Hakan dai na nuna yadda ‘yan takarar ke caccakar juna da kuma amfani da farfaganda wajen tallata kansu ga masu zabe.

Da yake sharhi akan wannan batu, Dr. Kabiru Sa’idu Sufi, Malamin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano ya ce, wannan tsari na amfani da farfaganda ya faro ne tun a shekara ta 2015, inda Jam’aiyyar hamayya ta yi amfani da wannan siga har ta ci zabe kuma ita-ma Jam’iyya mai mulki a wancan lokaci ta aminta cewa, an yi amfani da farfaganda ne wajen kawar da ita daga mulki.

Hakan ta sanya, in ji shi ‘yan siyasar Najeriya suka rungumi wannan akida ta farfaganda a zaben shekara ta 2019 kuma yanzu ma abin da suke yi kenan domin kai wa ga nasara.

Baya ga farfaganda, dukkanin Jami’iyyun sun bullo da tsarin ganawa ta musamman ga muhimman rukunan jama’a wa lau a shiyya ko jiha, kwatankwacin ganawar da Tinubu ya yi da ‘yan kasuwa da kuma Malaman addinin musulinci na shiyyar arewa maso yamma a Kano.

Dan takarar shugaban kasa na jami'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jami'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu

Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami’ar Bayero Kano, wanda ya yi tsokaci akan haka, ya ce hanya ce da ‘yan siyasar Najeriya ke ganin na da sauki wajen isar da sakon su ga ‘yan kasa, domin malamai da kungiyoyin matasa da na ‘yan kasuwa da makamantan, su nada tasirin gaske ga mabiyan su.

Sai dai Farfesan ya ce yayin da hukumomi ke kokarin hana amfani da kudi wajen neman kuri’a da kuma zabe, wannan hanya ta ganawa da rukunin mutane wata dama ce ta amfani da kudi a siyasa cikin sauki.

A ranar 25 watan gobe na Fabrairu ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa, kamar yadda yake kunshe a jadawalin zabukan bana da hukumar zaben Najeriya INEC.

XS
SM
MD
LG