‘Yan kasuwar yankin arewacin Najeriya na ci gaba da bayyana zullumi saboda barazanar da dukiyar su ke fuskanta, yayin da iyakokin Najeriya da Nijar ke ci gaba da zama a garkame biyo bayan takunkumin cinikayya da kungiyar ECOWAS karkashin shugaba Tinubu ta sanya akan Jamhuriyar ta Nijar .
Yayin da ake gudanar da gangami da bukukuwa domin fadakar da al’uma game da zagayowar ranar matasa ta duniya, da alama matasan a Najeriya sun fara nuna shakku kan yiwuwar shugabanni ka iya sama musu mafita dangane da kalubalen rayuwa da suke fama dashi.
Yayin da wa’adin rufe rijistar dalibai na bana a Jami’ar Bayero Kano ke cika, kungiyar tsoffin daliban Jami’ar lokacin tana karkashin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ta shiga tsakani.
Masu ruwa da tsaki a harkar kanana da matsakaitan masana'antu sun gana a Kano domin samo mafita akan matsalolin da suke hana 'yan kasuwa samun tallafi a arewacin Najeriya.
Taron masu ruwa da tsaki kan harkokin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu ya koka kan yadda mutanen lardin arewacin Najeriya ba sa samun damar cin gajiyar lamani da tallafin da gwamnatin tarayya, bankuna, cibiyoyin raya tattalin arziki kan bayar da nufin ciyar da tattalin arzikin al’uma gaba.
Biyo bayan zanga zangar lumana na rashin jin dadi game da halin kunci da al’umar kasar suka shiga, masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun fara mayar da martani dangane da nasara ko tasirin zanga zanga.
Mako guda bayan kaddamar da majalisar zartarwa a jihar Jigawa ta Najeriya, al’ummar jihar na ci gaba da dakon ji daga gwamnan jihar Malam Umar Namdi game da halin da lalitar jihar ke ciki.
Batun sammacin da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta ce ta aikawa tsohon gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana a gabanta don bada bahasi game da faifan bidiyon da ana ci gaba daukar hankalin kungiyoyi da ‘yan siyasa da kuma masu sharhi kan al’amuran yau da kullum a jihar ta Kano.
A wani mataki na dakile dabi’ar shaye-shaye da kallace-kallacen hotuna da fina-finan batsa a kafofin sadarwa na intanat na zamani tsakanin yara da matasa, wasu kamfanoni da cibiyoyi masu zaman kansu a jihar Kano suka shirya taron lacca domin fadakarwa.
‘Kasa da sa’o’I 24, tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani dangane da sammacin da hukumar yaki da rashawa da kula da korafin jama’a ta jihar ta ce ta aika masa ya bayyana a gabanta domin bada bahasi kan bidiyon da ake zargi ya nuna yana karbar cin hancin daloli
Kasa da makonni uku Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kwato filayen da darajar kudin su ta kai fiye da Naira Triliyon guda daga hannun mutanen da aka mallakawa ta haramtacciyar hanya.
Domin Kari