Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganduje Ya Mayar Da Martani Kan Bukatar Ya Bayyana A Gaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano


Tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

‘Kasa da sa’o’I 24, tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani dangane da sammacin da hukumar yaki da rashawa da kula da korafin jama’a ta jihar ta ce ta aika masa ya bayyana a gabanta domin bada bahasi kan bidiyon da ake zargi ya nuna yana karbar cin hancin daloli

KANO, NIGERIA - A hira ta kafar talabinjin na Channels a jiya Alhamis, shugaban hukumar yaki da rashawar ta Kano Barrister Muhuyi Magaji ya ce ya rattaba hannu akan wata takardar sammaci da aka aika wa tsohon gwamnan na Kano Abdullahi Umar Ganduje.

A cewar sa, a cikin wasikar, hukumar ta bukaci tsohon gwamnan ya bayyana a gabanta a makon gobe domin bada bahasi akan wanna faifen bidiyo na dala, biyo bayan binciken da hukamar ta ce ta fara akan lamarin, kasa da makonni uku da dawo da Barrister Muhuyi Magaji akan kujerar shugabancin hukumar.

Ya ce gabanin haka, hukumar ta tabbatar da sahihancin fefen bidiyon, wanda a baya can ake tababa akan ingancin sa.

Sai dai tsohon gwamna Ganduje ta bakin kwamishinan sa na harkokin raya karkara da ci gaban al’umma, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso ya mayar da martani dangane da wannan sabon yunkuri na hukumar yaki da rashawar ta jihar Kano.

Yana mai cewa,“Tun shekaru biyu zuwa uku da suka gabata mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mika wannan batu a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja kuma yanzu haka maganar tana kotu, don haka bai kamata ace wani ya yi sammaci ya ce yana bincike akan lamarin dake gaban kotu”

A hannu guda kuma, kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari sun fara tofa albarkacin bakin su game da batun, Inda Comrade Ibrahim Garba Maryam, mamba a zauren gamayyar kungiyoyin na jihar Kano ya ce.

“Abinda ya kamata mutane su gane shine lokacin da wannan abu ya faru shi gwamna yana da kariyar doka, yanzu kuwa babu wannan kariya don haka dole yanzu doka tayi aiki akan sa ayi bincike, amma idan za ayi bincike tilas ne ayi bisa adalci. Shi cin hanci da wanda ya bayar da wanda ya karba duk suna ciki, saboda haka ina wanda ya bayar din? Ina kamfanonin da suka yi aikin? Ya kamata a hada dasu.”

Baya ga kungiyoyin fararen hula, masu sharhi a fagen siyasa da harkokin yau da kullum a jihar ta Kano na ci gaba da bayyana fahimtar su akan lamarin.

Alhaji Jafar Sani Bello daya daga cikin masu fashin baki akan siyasa da al’amuran yau da kullum a Najeriya ya ce “Ni a gani na Muhuyi ya saki damar sa ta bincikar gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin kuwa al’amarin ya faru lokacin yana kujerar shugabancin hukumar Rashawa ta Kano, amma bai ce komai ba kuma daga bisani suka yi fada har gwamnan ya sauke shi daga kujerar. Don a yanzu ba zai iya yin adalci ba ga tsohon gwamnan saboda ta yuwu a akwai gilli a zuciyar sa”.

Tun a shekara ta 2018 ne aka fara ce-ce-ku-ce akan wannan fefen bidiyo wanda mawallafin jaridar kafar Intanet ta Daily Nigerian wato Jafar-Jafar ya fara kwarmatawa lokacin da ake tunkarar zaben 2019, koda yake batun ya lafa daga bisani, amma masu kula da lamura na ganin sake bude shafin maganar ba zai rasa nasaba da kammala wa’adin mulkin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba da kuma yadda siyasar Kanon ke ci gaba da daukar sabon salo.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Ganduje Ya Mayar Da Martani Wa Hukumar Yaki Da Rashawa Na Cewa Ya Bayyana A Gabanta.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG