KANO, NIGERIA -A Jihar Kano, kungiyoyin ma’aikata karkashin inuwar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar sun bi umurnin kungiyar ta kasa, inda mambobinta suka fita zanga-zangar lumana domin bayyana damuwa da halin kuncin rayuwa da ‘yan kasar ke ciki biyo bayan karin farashin albarkatun mai.
Gamayyar kungiyoyin ma’aikata da na dalibai ne yayin zanga zangar lumana ke ta hawa kujerar naki dangane da yadda gwamnatin Najeriya ke nuna halin ko-in-kula kan halin tsadar rayuwa da ‘yan kasar ke ciki wadda ya samo tushe daga karin farashin albarkatun mai sanadiyyar cire tallafin mai da gwamnati ta yi.
Comrade Kabiru Inuwa Shugaban Kungiyar kwadago ta NLC a Kano kuma jagoran gangamin ya ce, “wadannan abubuwa na janye tallafin man fetur bai tsaya a nan ba, an tafi kuma kasuwar hada-hadar musayar kudaden kasashen waje wadda ita ce kuma take jan linzamin farashin kayayyaki a kasuwanninmu, al’amarin da ya sanya darajar Naira ta fadi kuma al’umma suka shiga mummunan yanayi.”
A nasa banagaren, Comrade Mubarak Yerima jagoran kungiyar TUC ta ma’aikatan da ke aiki a cibiyoyi masu zaman kansu reshen jihar Kano, ya nanata cewa ba za su lamunce da yadda gwamnati ke yin biris da kuncin rayuwa ba, a don hakan zanga-zangar ta yau ita ce zango ko mataki na farko na yakar wannan akida ta gwamnati.
Ya ce, “kugiyar TUC ta baiwa gwamnati mako biyu akan cewa, lallai gwamnati ta fara zartar da dukkanin abubuwan da kwamitin hadin gwiwa na gwamnati da ‘yan kwadago suka amince da shi, amma sai bangaren gwamnati suka fara wani turanci kuma mu ba turanci ne a gabanmu ba, muna so ne mu gani a kasa.”
Ko da yake, ‘yan kwadagon sun yi shelar cewa, wannan zanga-zanga ta yau, ba ta nufin yajin aiki ba ce, amma bankuna da ofisoshin gwamnati, kasuwanni da cibiyoyin hada-hadar kasuwanci a Kano, sun kasance a kulle tun da safe har zuwa tsakar rana.
Sai dai daga bisani bayan sallar Azahar an bude kasuwanni yayin da zirga-zirgar ababen hawa ta ci gaba a sassan birnin da kewayen Kano, kuma ya zuwa yanzu jama’a sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, kamar yadda aka saba.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna