Rashin samun daidaito game da wanda zai jagoranci majalisar jihar ta Jigawa karo na takwas, shi ne ya haifar da tsaiko wajen rantsar da sabbin ‘yan majalisar ranar Talata.
A jihar Kano Najeriya, Hon Jibrin Isma’il Falgore ne ya zama shugaban majalisar dokokin jihar bisa amincewar daukacin ‘yan majalisar su 40. A wani kwarya-kwaryar biki na kaddamar da majalisar ta 10, sabon shugaban ya yi alkawarin tafiya tare da dukkanin ‘yan majalisar domin ciyar da jihar gaba.
Makiyaya da manoma a jihar Jigawa, Najeriya, sun fara tsokaci dangane da yarjejeniyar da hukumomin jihar da na Jihar Zinder a Jamhuriyar Nijar suka sanya wa hannu domin wanzar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyayan da ke zirga-zirga a sassan jihohin biyu da ke makwaftaka da juna.
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta shirya taron sanin makamar aiki a wani bangare na shirye-shiryen kaddamar da sabuwar Majalisar ta goma da za a gudanar ranar Talata makon gobe.
Sabon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi ya ce batun gudanar da garanbawul ga tsarin aikin gwamnati, shine mataki na farko da zai fara dauka kafin aiwatar da ajanda 12 na gwamnatin sa.
Bayan rantsuwar kama aiki, sabon gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce zai farfado da manufofi, tsare tsare da ayyukan gwamnatin jagoran Jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso.
Yayin da damina ke kankama a sassan Najeriya, Kungiyar Manoman shinkafa, sarrafa ta da kuma kasuwancinta ta Najeriya ta kaddamar da Shirin ta na bada lamunin kayan noma na musamman domin karfafa gwiwar manoma.
Bayan rantsar dashi a 29 ga Mayu, Ahmed Bola Tinubu na zaman shugaban Najeriya na 16, a daidai lokacin da yawan ‘yan kasar ya zarta miliyan 200.
Tun gabanin gudanar da zabukan da suka gabata a Najeriya batagarin matasa ke barazana ga mazauna birnin Kano ta hanyar kwace musu wayoyin, musamman a wasu yankuna na birnin walau da rana ko da daddare.
Al’umar jihar Kano gami da masu sharhi kan al’amuran yau da kullum a jihar na ci gaba da maida martani ga kalaman tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso na baya bayan nan dangane da makomar masarautun jihar bayan rantsar da sabuwa gwamnati.
Jinkirin bijiro da farashin kayayyaki ya jefa zukatan Manoma alkama a Najeriya cikin zulumi, al'amarin dake barazana ga makomar aikin noman alkamar a kasar.
Domin Kari